Jihar Kebbi na ci gaba da fuskantar tsananin hare-haren ƴan bindiga babu kakkautawa a cikin waɗannan kwanaki.
A wani rahoto da ya bayyana rabar Talata ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda 6 a harin da suka kai garin Ngaski dake jihar sannan sun kashe wasu jami’an ƴan sanda 4 a garin Gafara.
Wani mazaunin garin Lawal Magaji ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun aiko da wasika cewa za su kawo hari wannan gari da wani kamfanin sarrafa tumatirin gwangwani dake Gafara ranar Talata.
Ƴan bindigan ba su fasa ba kuwa domin a wannan rana suka shigo garin suka rika harbi ta ko-ina babu ƙakkautawa sun kashe wasu, wasu kuma sun tsira da rauni
Da suka isa kanfanin sarrafa timatir ɗin sun iske jami’an tsaro inda suka yi ta batakashi a tsakanin su.
An kashe ƴan sanda sannan sun yi awon gaba da mutane da dama.
Ance kafin su fice daga garin Ngaski sai da suka afka wani babban shagon sai da kayan masarufi suka saci kayan abinci da da sauran su sannan suka nausa cikin daji.
Ɗan majalisan dake wakiltan Yawuri, Shanga, Ngaski, Yusuf Tanko -Sununu ya ce lokacin da aka aiko da wasikar an kwashe ma’ikatan wannan kamfani gudun kada wannan hari ya ritsa da su.