Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya ƙundumbalar sayen fam ɗin takarar shugabancin APC na ƙasa, duk kuwa da cewa tsarin karɓa-karɓar APC ya tabbatar da cewa daga Shiyyar Arewa ta Tsakiya za a fito da shugaban APC cikin ƙarshen watan nan.
Shin za a ce ƙundumbala ce ko ƙumumuwa, karambani, kankanba ko kangara ce wannan Yari ya nuna kenan.
Cikin makon jiya APC ta tabbatar da cewa daga tsakanin jihohin Benuwai, Filato, Nasarawa, Neja da Kogi, Kwara ko FCT Abuja shugaban APC zai fito.
Wannan mataki kuwa ya datse guyawun wasu ‘yan takara aƙalla bakwai waɗanda ba a wannan shiyya ta Arewa ta Tsakiya su ka fito ba.
Jihar Zamfara inda Yari ya fito ba ta ciki Arewa ta Tsakiya, ta na Arewa maso Yamma.
Duk da haka sai ga Yari ya bayyana a Hedikwatar APC a ranar Laraba, inda ya karɓi fam na fitowa takarar.
APC dai ta na sayar da fam ɗin takarar shugabancin jam’iyya Naira miliyan 20, na mataimakin shugaba Naira miliyan 10. Na sauran muƙaman kuma naira miliyan 5 kowane.
Magoya bayan Yari, waɗanda suka yankar masa fam ɗin na ƙarƙashin Tijjani Ƙaura, Sanata mai wakiltar Zamfara ta Arewa a yanzu haka.
A Hedikwatar APC, Sanata Ƙaura ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu ba a daddale kan lallai daga yankin Arewa ta Tsakiya za a fito ko za a zaɓi sabon shugaban APC ba.
Waɗanda su ka sayi fam sun haɗa har da Salihu Mustapha da Abdullahi Adamu.
Premium Times Hausa ta balarin da Sanata Abdullahi Adamu ya ce ‘daga sama aka ce min na fito takarar shugabancin APC”.
Tsohon Gwamnan Jihar Nassarawa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa wasu manya kuma ƙusoshin jam’iyyar APC ne su ka ce ya fito takarar shugabancin jam’iyyar.
Adamu ya yi wannan bayani a ranar Talata, lokacin da ya ke ganawa da Mambobin Tarayya ‘yan APC a Abuja.
Bayanin sa ya zo daidai lokacin da ake watsa rahotannin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fi son Sanata Adamu ya zama shugaban APC na ƙasa.
Adamu ya ce shi ne na ƙarshen fitowa ya bayyana aniyar sa ta neman shugabancin APC, saboda sai da ya jira ya samu umarni daga ƙusoshin jam’iyyar masu faɗa a ji.
Ya yi nuni da cewa bai kamata mai neman shugabanci ya nuna maitar sa a fili ba, kamata ya yi ya jira, har sai an kira shi an ce masa ga ragamar shugabanci ka riƙe tukunna.
Adamu wanda kwanan nan ya shugabanci kwamitin sasanta hasalallun APC da masu rigima a cikin jam’iyyar, ya ce wannan gagarimin aiki da aka ba shi ya taimaka masa wajen gani da kuma sanin matsalolin da suka dabaibaye APC.
Ya cecya karɓi tayin fitowa neman shugabancin APC ne saboda ya na girmama mutanen da su ka ce ya fito takara.
“Saboda sun yarda sun amince cewa na fi cancantar riƙe APC, don haka na fito takara za su zaɓe ni. Daga nan na tuntuɓi waɗanda su ka dace na tuntuɓa, sai na fito kawai.” Inji shi.
Ban Taɓa Faɗuwa Zaɓe Ba Tun Daga 1978 Har Yau -Sanata Adamu:
Da ya ke magana kan yadda zai riƙe jam’iyyar, Adamu mai wakiltar Mazaɓar Sanatan Nasarawa ta Yamma, ya ce tun daga 1978 har yau bai taɓa faɗuwa zaɓe ba. Don haka ya fahimci dukkan ƙalubalen da ke fuskantar APC.
“Na naƙalci yadda ake zaɓe, yadda ake tafiyar da zaɓe, matakan da ake ketawa kafin a yi zaɓe da sauran su.
“Daga 1978 har zuwa yau, ban taɓa shiga takara na faɗi ba. Don haka ina da yaƙin cewa idan aka ba ni shugabancin APC, zan yi wa jam’iyyar kyakkyawan riƙon da za ta daɗe ta na riƙe da akalar gwamnati a ƙasar nan.
Abdullahi Adamu: Yadda Mai Kashi A Wando Ke Neman Shugabancin APC:
Abdullahi Adamu ya yi gwamna tsawon shekaru takwas, daga 1999 zuwa 2007 a jihar Nasarawa. Daga nan kuma ya zarce Majalisar Dattawa, inda har yau bai faɗi zaɓe an kayar da shi ba.
Cikin 2010 an gurfanar da shi a kotu, inda aka zarge shi da wawurar naira biliyan 15.
Har yau ba a san matsayin da wannan tuhuma da ake yi masa ke ciki ba.
Amma a cikin 2016, Adamu ya taɓa an kori ƙarar da tuhumar da ake yi masa ce, shi ya sa aka ji tsit.
Lokacin da Bukola Saraki ke Shugaban Majalisar Dattawa, an tsige Adamu daga Shugaban Kungiyar ‘Yan Majalisar Dattawan Arewa, saboda an zarge shi da yin rub-da-ciki kan wasu maƙudan kuɗaɗe.
Kwanan baya a wata hira da aka yi da Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, ya ce Shugaba Buhari ya ce a zaɓi wani ɗan Arewa ta Tsakiya a matsayin shugaban APC. Amma bai ambaci sunan sa ba.
Discussion about this post