Sarkin Kano na 14, kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya roƙi mabiyan addinai daban-daban su rungumi juna, kuma su riƙa haƙurin zamantakewa da juna.
A ɗaya gefen kuma, Khalifan na mabiya Ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya ya jinjina wa mabiya addinin da ba musulunci ba, saboda karɓar da suka yi wa tsarin bankin Musulunci hannu bibbiyu.
Khalifan ya yi wannan jawabi a Legas ranar Lahadi, a lokacin da ya halarci taro matsayin sa na Babban baƙo na musamman a wurin taron ƙasa na 5 don tattaunawa kan harkokin kasuwancin tsarin Musulunci, wanda masana da ƙwararru musulmai suka shirya a Legas.
Taron mai taken: “Tsarin Banki da Kasuwancin Islama A Najeriya: Riba, Ƙalubale da Nasarori”, an gayyato masani kuma farfesan Shari’ar Muslunci a Jami’ar Ilorin, AbdulRazaq Alaro, a matsayin babban baƙo mai jawabi.
Sanusi wanda ya haƙaito tarihin kafa Bankin Musulunci a Najeriya, kuma ya bada labarin irin gwagwarmaya da sukar da tsarin ya sha daga bakin mutane daban-daban, har da shugabannin addinai, ya gode wa wasu da ba musulmai ba, saboda goyon bayan da suka bayar har CBN a lokacin mulkin sa ya fita daga tarkon duk wani ƙalubalen da ya fuskanta.
Sanusi ya shawarci Musulmai to tabbatar a koda yaushe su na riƙe amanar abokan su da ba Musulmai ba.
Daga nan ya nuna cewa riƙe misalin wani mutum ɗaya a matsayin ra’ayin sa ko fahimtar sa ita ce ra’ayin baki ɗayan ra’ayin ƙabilar sa ko mabiya addinin sa, wannan ba hujja ko adalci ba ne.
Ya ce da yawan mutane sun gani kuma sun san alfanu da fa’idojin Bankin Musulunci, amma saboda dalilai na addini, sai idon su ya rufe.
Sanusi ya yi kira ga Babban Bankin Najeriya (CBN) ya haɗa guiwa da Cibiyar Horas da Alƙalai ta Kasa (NJI) domin ta horas da Masu Shari’a a ƙasar nan dangane da ƙabali da ba’adin da ke tattare da tsarin Bankin Musulunci.