Kamfanin Multichoice ya ce sabon farashin kallon zai fara aiki ne daga farkon watan Afirilu.
MultiChoice ya ce daga ranar 1 ga Afrilu wadanda suke kallon DSTV ‘premium bouquets’ za su rika biyan naira 21,000 daga naira 18,400, da suke biya a baya. Sannan masu amfani da ‘Compact Plus’ za rika biyan Naira 14,250 daga Naira 12,400 sannan masu amfani da ‘Compact’ za su rika biyan 9,000 daga Naira 7,900.
Masu amfani da ‘Confam’ za su rika biyan Naira 5,300 daga Naira 4,615 sannan masu amfani da ‘Yanga’ za su biya Naira 2,950 daga Naira 2,565.
Kamfanin ta ce ta yi wannan kari ne saboda yadda farashin komai ya karu.
Karin da Kamfanin ya yi ya zo bayan an yi kwanaki biyu da gwamnatin tarayya ta umurci kamfanin ta rika barin mutane suna biyan farashi daya na akalla shekara daya kafin su canja farashin.
Gwamnati ta umurci kamfanin da ya rika bai wa mutane damar dakatar da kudaden da suke biya akalla sau hudu a shekara.
Kamfanin za ta bada lambobin waya wanda mutane za su iya kira da kowace irin layin sadarwa kyauta domin korafin ko neman taimako.
Bayan haka kamfanin ya ce zai amince wa mutanen da suke biyan kudaden su da su ci gaba da biyan tsohon farashin da suke biya idan sun amince za su ci gaba da biyan kudaden su da wuri na akalla tsawon shekara daya.