Jami’an Tsaron Sirri na SSS sun bayyana cewa sun bankaɗo wani shirin tayar da tashin hankali a wasu yankunan Najeriya, musamman ma a Tsakiyar Najeriya.
SSS sun bayyana haka a cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na rundunar, Peter Afunanya ya fitar a ranar Asabar. Sanarwar ta ce masu ƙoƙarin shirya tarzomar na son yin maye-fake-da-annoba, wato fakewa da matsalar wutar lantarki su tada tarzomar.
DSS sun fallasa tuggun a daidai lokacin da matsalar wutar lantarki da kuma matsalar fetur wadda ta yi ƙamari tun a farkon Fabrairu.
An dai fara shiga matsalar ce a farkon sabuwar shekara, tun daga shigo da gurɓataccen fetur daga Belgium.
Ƙarancin fetur ɗin ya haifar da dogayen layukan sayen fetur a gidajen mai ɗin faɗin ƙasar nan, sannan kuma ya haifar da tsadar sa.
Lamari ba a fetur kaɗai ya tsaya ba, har da man dizal, wanda a yanzu litar sa ɗaya tai naira 720.
Lalacewar tashoshin samar da hasken lantarki ya haifar da matsalar wuta da makamashi a Najeriya baki ɗaya.
A cikin sanarwar DSS, sun ce waɗanda ke son tayar da rikicin sun yi niyyar amfani da ɗaliban jami’o’i da na sauran manyan makarantu da kuma malaman jami’o’i, waɗanda a yanzu ke zaune gida saboda yajin aikin da ASUU ke ci gaba da yi.
“Rundunar Tsaro ta DSS na sanar da cewa sun bankaɗo wani shiri da wasu ɓatagari ke yi domin don tayar da hargitsi cikin ƙasar nan, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya.
“Ƙoƙarin su shi ne haddasa rikicin addini da na ƙabilanci, daga nan sai waɗanda aka ƙwarya kuma sai a zuga su domin su ɗauki fansa, sai ƙasa ta dagule, yadda batun siyasa zai ƙara zafi sosai.
“A ƙoƙarin cimma wannan mummunar manufa ta su, sun gudanar da taruka a ciki da wajen wuraren da su ke so su tayar da rigingimun.
“Kuma DSS na sane da ƙoƙarin da su ke yi ta hanyar yin amfani da ɗalibai da malaman jami’o’i, ƙungiyoyin kishin jama’a, Kungiyoyin Ƙwadago da kuma tantagaryar ɓatagari, domin shirya tarzoma makammanciyar irin ta #EndSARS.
DSS ta ce babu ruwan waɗannan mutane da duba ƙoƙarin da gwamanti ke yi domin kawo ƙarshen matsalolin.”
Daga nan DSS ta ja hankalin masu wannan mummunan shiri cewa su shiga taitayin su.
Discussion about this post