Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa cewa su tashi tsaye haiƙan su karɓi kuɗaɗen haraji a hannun jama’a, domin su ƙara samun kuɗin shiga.
IMF ya ce idan aka ƙara tatsar haraji daga albashi da sauran hanyoyin kuɗaɗen shigar mutane ɗaiɗaiku, zai ƙasa samar wa ƙasashen kuɗin shiga sosai.
IMF wanda ke da hedikwata a Washington, ta ce ƙara tatsar haraji daga hannun jama’a zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin su, musamman ganin yadda tattalin arzikin su ya durƙushe a lokacin korona. IMF ya ce Harajin Jiki Magayi ya na da alfanu wajen bunƙasa tattalin arziki.
Haka kuma IMF ya ce akwai buƙatar a ƙara sa-ido wajen tafiyar da yadda ake tara kuɗaɗen, domin hakan ya na ƙara alkinta kuɗaɗen da aka tara, har ma da wasu fannonin tara harajin na daban.
Sannan kuma IMF ya ƙara da cewa gaggauta komawa a tsarin karɓar haraji na zamani zai ƙara inganta tattalin arziki ga kasashe masu tasowa.
Ko a cikin watan Nuwamba 2021 sai da Bankin IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin mai da na kuɗin wutar lantarki a farkon 2022.
Idan Gwamnatin Najeriya ta yi amfani da shawarar Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) har ya cire tallafin man fetur da na wutar lantarki a farkon 2022, ‘yan ƙasar nan za su shiga sabuwar shekara cikin halin ƙuncin rayuwar da ta fi ta shekarar 2021 da ake ciki.
Kai tsaye ba wani abu ba ne cire tallafin man fetur da na wutar lantarki, ma’ana ita ce a ƙara wa farashin litar man fetur da wutar lantarki kuɗi.
IMF ta gargaɗi Najeriya cewa yawan kuɗaɗen da ta ke kashewa idan auna su da waɗanda ta ke samu, to za’a ci gaba da samu wawakeken giɓi a kowace shekara, kamar irin wanda aka samu a bana cikin 2021, to haka ma za ta kasance a shekara mai zuwa.
“Amma idan aka cire tallafin fetur da na kuɗin lantarki, an kamo hanyar saisaita matsalolin ƙaranci kuɗi a hannun gwamnati kenan.
“Amma kuma tilas sai ita gwamnatin ta bijiro wasu tsare-tsaren da za ta rage wa talakawa tsadar rayuwa, sakamakon matsin da za su shiga idan an ƙara kuɗin fetur da kuɗin wutar lantarki. Kuma dama akwai wannan sharaɗin a cikin Sabuwar Dokar Man Fetur ta 2021 cikin watannin baya.”
IMF ya ƙara da cewa, tafiyar-hawainiyar da sabon tsarin canjin kuɗaɗe ke yi, tare da rashin tabbas na kasa maido maƙudan kuɗaɗen da ɓarayin gwamnati su ka sace suka ɓoye a waje, ya rage ƙarfin yawan shigowar jari mai nauyi a Najeriya.”
Wasu ƙarin matsalolin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da fuskanta, a cewar IMF, sun haɗa da ƙarancin kayan da Najeriya ke fitarwa waje.
A kan haka sai IMF ta nemi Najeriya ta fito da wani tsari da zai daɗe tsawon lokaci ya na hana kuɗaɗen ajiyar Najeriya a waje raguwa.