Na daɗe ina yin dubi ga yadda siyasar Kaduna za ta kasance a 2023. Babban abinda ke bani tsoro da mamaki shine yadda na ga makusantan gwamnan jihar Nasir El-Rufai ke rige-rigen maye gurbinsa idan wa’adin mulkin sa ya cika a 2023.
Abinda za ka ji mutane na tattaunawa a kowani majalisi shine shin wanene gwamna El-Rufai zai mara wa baya a Kaduna?
Mazauna jihar Kaduna sun san yadda dukka ƴan takaran da suke da gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i.
Da farko dai a matsayina na manarzancin siyasa a jihar, zan iya cewa a wannan karon El-Rufai ya na neman ya gwara kan ƴan Kaduna ne .
Da farko dai bari mu bi ƴan takaran daya bayan daya musamman Malam Uba Sani da Mohammed Abdullahi, Dattijo.
Duk wanda ya san gwamna Nasir El-Rufai, tun daga 1999 zai ce maka tare ya gan su da Sanata Uba Sani. Sun yi aiki tare a lokacin shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Haka kuma ko a lokacin da gwamna El-Rufai ya zama gwamnan Kaduna ya naɗa Uba Sani babban mai bashi Shawara kan harkokin siyasa a jihar. Mukamin da ya rike tun daga 2015 zuwa 2019.
A shekarar 2019 kuma sai Uba ya garzaya majalisar Dattijai domin wakiltar Kaduna ta tsakiya. Muƙamin da sai da aka kai ruwa rana tsakaninsa da Sanatan dake kai a lokacin wato sanata Shehu Sani.
Abin saida ya kai ga kamar da wuya, bayan gwamna El-Rufai ya fallo takobinsa cewa ko dai APC ta mika wa Uba tikitin kujerar Sanata ko kuma ta ɓare.
Daga karshe dai Uba ne sanatan Kaduna ta tsakiya.
Kowa ya san a duk lokacin da kaga Sanata Uba Sani to ya fito aiki ne, aikin kuma bai wuce na gyara wa gwamna El-Rufai tukunyar miyar sa ba, ya cigaba da samun yadda yake so da ƴan siyasa a Kaduna sannan mulkin sa ta yi kyau.
Haka shima matashi Mohammed Dattijo, shima dai sarkin yakin El-Rufai ne a Kaduna.
Tun a 2015 da aka kafa gwamnati, Dattijo ke aiki karkashin gwamnatin El-Rufai daga kwamishina zuwa rike muƙamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna.
Sai dai kuma wani abu da ake lissafida shi a wannan tafiya na makusantan gwamna El-Rufai shine, a kusan kowani fanni a siyasance, Uba Sani ya Dattijo gogewa.
Sannan ana ganin duk irin goyon bayan da zai samu daga gwamna El-Rufai ba zai iya yin tasirin kada PDP ba a jihar Kaduna.
Yanzu ne jama’a suka san shi a siyasance, duk da ko mahaifiyarsa gogaggiyar yar siyasa ce a jihar Kaduna, wato Honarabul Saudatu Sani.