Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta sallami tsohon Shugaban Hukumar NNPC, Andrew Yakubu daga zargin satar dala miliyan 9.8 ɗin da aka samu a gidan sa na Kaduna, cikin 2017.
Cikin 2017 ne EFCC ta yi wa gidan sa na Kaduna dirar-mikiya a unguwar Sabon Tasha, Kaduna inda aka bankaɗo dala miliyan 9,772, 200 da kuma fam 74,000 na Ingila.
Daga nan ne EFCC ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Ahmed Mohammed a Abuja, inda aka tuhume shi da laifuka shida masu nasaba da karkatar da kuɗaɗe.
Amma kuma hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke, ta soke hutuma uku, an bar uku kaɗai.
Yanke Hukunci: A ranar Alhamis Mai Shari’a Mohammed ya ce lauyan EFCC ya kasa gabatar da hujjojin da za a iya kama Andrew Yakubu da laifin da har za a ɗaure shi.
“Hujjojin da Andrew Yakubu ya gabatar domin kare kan sa abin dogaro ne, kuma sahihai ne.
“EFCC ta kasa gabatar da shaidar da za ta kifar da hujjojin da Andrew Yakubu ya gabatar, kamar yadda doka ta tanadar.”
Mai Shari’a Mohammed ya ƙara da cewa kamata ya yi EFCC ta yi ƙwaƙƙwaran bincike domin gamsar da kotu cewa ƙarya Andrew Yakubu ya ke yi, da har ya ce kuɗaɗen abokan sa ne su ka ba shi kyauta.
“Amma abin takaici, sai EFCC da lauyan EFCC su ka kasa yin hakan. Su kaɗai su ka san dalilin kasa tabbatar da hujjojin su.
“Sannan kuma EFCC ta sun ce Yakubu ya kwashe kuɗaɗen a lokaci ɗaya ne ya ɓoye a gidan sa. Shi kuma ya ce abokai ne daban-daban su ka yi masa kyautar kuɗaɗen cikin 2014.
“Gaskiyar magana dai EFCC ta ɗibga babban kuskuren kasa gabatar da sahihan hujjoji ko shaidu, sai bayan da ita da kan ta ta kammala shigar da hujjojin ta, sannan ta nemi shigo da wani ba’asi daban kuma.
“Baki ɗaya hujjojin Yakubu sun sanya kotu na tababar shaidun da EFCC ta gabatar. Don haka dole shi a daina tababar hujjojin kare kan sa da ya gabatar.”
Mai Shari’a ya yarda cewa kuɗin duk kyauta ce abokai su ka ba shi daban-daban, ba a lokaci ɗaya ba.
“Da a lokaci ɗaya ne aka ba shi kyautar kuɗaɗen, to da tilas Dokar Laifin Karkatar da Kuɗaɗe ta 2011 ta hau kan sa.
A ƙarshe kotu ta wanke Andrew Yakubu fes, tare da cewa iƙirarin da EFCC ta yi cewa an karya doka wajen tara kuɗaɗen saboda ba su biyo ta banki ko bankuna ba.
Discussion about this post