Hukumar kare hakin dan Adam ta ƙasa NHRC ta bayyana cewa ta saurari kararrakin cin zarafin mata da yara kanana 158,517 a Najeriya a shekararp 2021.
Shugaban hukumar Tony Ojukwu ya sanar da haka a taron da gidauniyar ROOST da NHRC suka shirya kuma aka yi a Abuja ranar Litinin.
Taken taron shine “Tattauna karuwa da ake samu na cin zarafin mata da yara kanana da kirkiro matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar”.
“Hukumar ta saurari kararraki 913,197 a shekarar 2021 inda a ciki ta saurari kararrakin cin zarafin mata da yara kanana 158,517.
Ojukwu ya ce kafa kwamitin shugaban ƙasa domin gudanar da bincike kan kararrakin cin zarafin mata da yara kanana da bude layin waya domin kawo kara na daga cikin matakan da aka tattauna a taron domin kawo karshen matsalar a kasar nan.
Lokaci ya yi domin daukan mataki
Bayan haka ministan al’amuran mata da yara Pauline Tallen ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada hannu da gwamnati wajen ganin an kawo karshen cin zarafin mata da yara kanana.
Ta yi kira ga mutane da su hada hannu da mata wajen yin addu’o’i tare da jawo hankulan maza kan sanin illolin dake tattare da cin zarafin mata da yara kanana.
Wacce ta shirya taron Julie Okah-Donli ta bayyana cewa an shirya taron ne domin gano matsalolin dake tattare da cin zarafin mata da yara kanana domin samar da matakan da za su taimaka wajen kawar da su.
Julie ta yi kira ga masu ruwa da tsaki musamman hukumar NAPTIP da su hada hannu domin yakan wannan matsala a kasar nan.