Yadda kawai mai kamatu zai fi sauƙin fahimtar wannan bayani, shi ne a ce masa: Cikakken bayani ne kan yadda wauta da gangancin Shugaban Ukraniya Volodymyr (Waldima) Zelensky ya biye wa Amurka, ta kai shi cikin garken kuraye ta gudu ta bar shi.
1. An zaɓi Volodymyr Zelensky cikin 2019 a zaɓen da ya yi gagarimar nasara, saboda ya yi alƙawarin shi ne zai iya kashe wutar da ke neman tashi tsakanin Ukraniya da Rasha.
2. Zelensky a wurin kamfen ya kuma yi alƙawarin magance rikicin cikin Ukraniya, wanda wasu yankunan cikin ƙasar da ke Gabas su ka ɓalle.
Shi wannan yanki da ya ɓalle, al’ummar cikin sa ƙabilar yaren Rasha ne, kuma sun yi maƙwautaka da Rasha ɗin.
3. Amma bayan zaɓen Zelensky, ko sau ɗaya bai taɓa yin ƙoƙarin sasanta rikici da Rasha ba ko rikicin cikin Ukraniya.
Fatali Da Yarjejeniyar Minsk:
4. Maimakon ya sasanta, sai Zelensky ya tashi haiƙan ya na dangwalar hancin Rasha da tsinin mashi. Ya samu damar zama da Rasha su warware rigingimu a kan teburin shan shayi, amma sai ya yi biris.
5. Me Zelensky ya koma yi? Sai kawai ya riƙa bin shawarar Amurka da umarnin ta ido-rufe.
6. Zelensky ya kasa gane cewa zaman lafiya da Rasha ne kaɗai mafita ga Ukraniya, amma ba ƙulla ƙawance da Turawan Yamma da Amurka ba.
7. Zelensky ya hau mulki ya iske Yarjejeniyar Birnin Minsk na Belarus. Maimakon ya kiyaye yarjejeniyar, sai Zelensky ya yi fatali da ita.
8. Hakan ya ƙara rura rikicin ƙabilancin da dama ya faru tun shekaru takwas kafin hawa
mulkin Zelensky.
9. Putin ya gano take-taken Zelensky, har ya riƙa yi masa gargaɗi a fakaice, ya na cewa: “Kun dai gani ko, Shugaba Zelensky ya yi fatali da Yarjejeniyar Minsk. To ai wanda ya ƙi ji, ba zai ƙi gani ba!”
10. Duk manyan ƙasashen duniya sun san yin fatali da yarjejeniyar Minsk da Zelensky ya yi, bayan Rasha ta jure bin yarjejeniyar tsawon shekaru takwas, shi ya ƙarasa harzuƙa Rasha afkawa Ukraniya.
11. Wa ya zuga Ukraniya yin fatali da Yarjejeniyar Minsk? Amurka ce, kowa ya sani.
Gangancin Ukraniya Na Girke Dakaru 60,000 A Yankin Gabas, Cikin Ƙabilar Rashawan Ukraniya:
12. Zelensky wanda ya yi alƙawarin kawo zaman lafiya da haɗin kan ƙabilu, maimakon haka, sai ya girke dakaru 60,000 a yankin gabas mai maƙautaka da Rasha, kuma akasari ƙabilar Rashawa ne a yankin.
Bayan wanann kuma sai ya riƙa shigo da makamai da Amurka da Turai ta Yamma. Ya ayyana fara shirin tanadar makamashin nukiliya. Ya yi fatali da yarjejeniya. Shin Rasha za ta zuba masa ido? A’a.
14. Zelensky ya yi kuskuren tura dakaru 60,000 yankin gabas mai ƙabilun Rashawa. Ta kai ana kai masu hare-haren neman shafe su. Wanda kuwa Rasha ba za ta taɓa amincewa Ukraniya ta shafe ‘yan ƙabilar ta da ke Ukraniya ba, kuma kan iyaka da Rasha.
15. Me Zelensky ke nufi da ko son cimmawa idan ya kakkaɓe Rashawan Ukraniya? Ya na jin Rasha za ta zuba masa idanu ya murƙushe ‘yan ƙabilar ta? A’a.
16. Shin tashin hankali Zelensky ya nema da Rasha ko zaman lafiya? Tashin hankali ya nema!
Rasha Ta Tura Dakaru 200,000 Ita Ma:
17. Ganin take-taken Zelensky, sai Vladimir Putin na Rasha ya fusata, ya tura dakaru tare da muggan makaman da duk duniya ta firgita da su, domin su kare Rashawan da suka ɓalle daga Ukraniya, waɗanda Zelensky na Ukraniya ke neman shafewa.
Babban Kuskuren Ukraniya Kan Neman Shiga Ƙungiyar NATO:
18. Babu yadda za a yi Rasha ta bari Zelensky na Ukraniya ya tattago NATO ya kawo har kan iyakar ƙasar Rasha. Shi ma ya san haka.
19. Zelensky ya sani sosai tun cikin 2014 Putin na Rasha ke nanata cewa Rasha ba za ta taɓa bari NATO ta kafa sansani a Ukraniya ba. “Sai dai a yi wadda za a yi. Sai dai Turai baki ɗaya ta yi baram-baram!”
20. Me ya sa Zelensky ke son kawo NATO a Ukraniya, ƙungiyar da ke neman ganin bayan Rasha a duniya?
21. Shin Zelensky bai san NATO ta ruguza Yugoslavia da Afghanistan da Syria da Libiya ba? Ya sani.
22. Shin Zelensky ya san NATO ba ta son Rasha, kuma ba ta son mai son Rasha? Ya sani. Shin wa ke zuga shi? Amurka.
Hujjar Rasha Kan Mamaye Ukraniya:
23. Maimakon Zelensky ya cika alƙawarin shinfida tabarmar zaman lafiya da Rasha da kiyaye yarjejeniyar Minsk, sai ya fara shirin tanadin makaman nukiliya.
24. Idan Amurka da Turawan Yamma suka ɗaure masa gindi ya tanadi makaman nukiliya, wace ƙasa zai ruguza? Rasha mana! Shin Rasha za ta ƙyale Ukraniya ta tanadi nukiliya? A’a.
25. Dalili kenan a fakon yaƙin Rasha ta gaggauta ƙwace tashar makamashin nukiliya ta Ukraniya.
Misalin Ukraniya Da Rasha, Kamar Misalin Amurka Da Mexico Ne:
26. Shin Amurka za ta bari maƙauciyar ta Mexico ta ƙulla ƙawance makamai da Rasha? A’a.
27. Shin Amurka za ta bari Mexico ta mallaki makaman nukiliya? A’a.
28. Shin Amurka za ta yarda da dakarun Rasha a Mexico ƙofar hancin Amurka? A’a.
29. Tunda Zelensky ya san da haka? To tabbas kuwa ya san Rasha ba za ta bari ya tattago NATO da Amurka zuwa Ukraniya ba. Sai dai Turai ta hargitse.
Ɓullar Aƙidar NAXI Magoya Bayan Hitler A Ukraniya:
30. Zelensky ya sani sarai a Ukraniya wata ƙungiya mai yaɗa aƙidar Hitler, kuma ta yi ƙarfi har a cikin gwamnati.
Ko a cikin
2014 mabiya ƙungiyar sun ƙone mutum 40 ƙurmus a Cibiyar Trade Union da ke Odessa.
Wannan ƙungiya ta tashi haiƙan wajen yaɗa ƙiyayya kan ƙabilar Rashawan Ukraniya da tsangwamar su.
Putin na Rasha ya san CIA na bai wa mayaƙan sunƙuru horo a asirce a Ukraniya.
Rasha Ba Ta Manta Kisan-kiyashin Da Dakarun Hitler Suka Yi Wa Rashawa A Yaƙin Duniya Na Biyu Ba:
31. Ɓullar ‘yan aƙidar Hitler masu tsanar Rashawa a Ukraniya ya tashi hankalin Putin na Rasha. Shi da kwamandojin sa ba za su taɓa manta tarihin Yaƙin Duniya Na Biyu ba, wanda Sojojin Hitler suka kashe sama da al’ummar Rasha miliyan 20.
Don haka Putin ke ganin da ya zauna turus a kassara Rasha, gara ya tashi a-yi-ta-ta-ƙare kawai.
Bahaushe dai ya ce ‘mai rabon ganin baɗi, sai ya gani.’
Shi kuma mawaƙi Kassu Zurmi cewa, “mutuwa ta raina mai gajeren kwana.”
Discussion about this post