A yau Asabar ne aka ɗauren gimbiya Firdauz Abdullahi Bayero da Sarkin Iwo dake jihar Osun a birnin Kano.
Ɗaurin aure ya samu wakilcin mataimakin shugaban Kasa da manyan hakimai da masu sarautu a birnin Kano.
An ɗaura auren a gidan Madakin Kano sannan kuma angon Firdauz sarkin Iwo Adewale Akanbi (Telu 1) ya biya sadakin naira miliyan 1 lakadan.
Mahaifin Firdauz Abdullahi Sarki Sani Yola wanda shine Madakin Kano na 15 ya rasu a shekarar 2008.
Gimbiya kuma sarauniya Firdauz ta yi karatu a birnin Kano kuma yanzu tana da shekaru 27 da haihuwa.
Discussion about this post