Dan majalisar Tarayya dake wakiltar Damboa/Gwazo/Chibok ya bayyana cewa jami’an tsaro sun maida harkar rashin tsaro sana’a da ake samun kudi masu yawa a cikinsa a kasar nan.
” Ku duba irin kudaden da muke warewa harkar tsaro a kasafin kudin kasar nan. Tun daga 2020 ake ware wa fannin tsaro na sojojin kasa kawai biliyoyin nairori. Me suke yi da shi. Idan wannan ya kwashi nashi, wancan shima zai ce sai ya kwashi nashi kudin. Abin ya zama sana’a babba yanzu. Ba za su taba bari a kawo karshen sa ba.
” Abinda na sani shine yanzu sun canja salo, sun dawo yankin Arewa Maso Yamma, daga nan kuma za su nausa wani yankin idan ba a maida hankali a kai ba.
A bari ‘yan Najeriya su mallaki makamai
Shugaban masu rinjaye na majalisar Tarayya Honarabul Ado Doguwa ya kalubalanci gwamnatin tarayya ta kyale ƴan Najeriya su mallaki bindigogi domin kare kansu.
Da ya ke tofa albarkacin bakin sa a mahawarar da aka yi a zauren majalisar ranar Alhamis, Doguwa ya ce lalacewar ta yi yawa yanzu kuma abin ya fi ƙarfin gwamnati yanzu.
” Kai a kyale mutane su mallaki makamai kawai su kare kansu domin gwamnati ta gaza, jami’an tsaro sun gaza. Babu yadda za a yi a buɗa kawai duk wanda ya far maka ka kare kanka.
Duk da cewa shine shugaban nasu rinjaye na majalisar kuma Doguwa bai gaza ba wajen faɗin gaskiyar halin da matsalar tsaro ta ke ciki a kasar nan.
” Idan jami’an tsaro sun gaza, bai kamata dukkan ‘ƴan kasa su afka cikin wannan bala’i ba, a kyale kowa ya mallaki makami. A haɗa kungiyoyi a rika tunkarar duk wanda ya doso mutane da bala’i.
Idan ba a manta ba a cikin farkon wannan mako ne ƴan bindiga suka tada bam a layin dogon jirgin kasa daga Abuja-Kaduna.
An kashe mutum 8 sannan da dama an yi garkuwa da su har yanzu suna tsare a hannun ƴan bindigan.
Jihar Kaduna na cikin halin tsaka mai wuya ganin yadda hare-haren ƴan bindiga ya tsananta a ƴan kwanakin nan.
Discussion about this post