Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana harin da ‘yan bindiga su ka kai wa jirgin ƙasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna, cewa ya yi muni matuƙa, kuma abin damuwa ne.
Buhari ya bayyana haka cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran sa Garba Shehu ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
“Ba za mu bar wasu ‘yan ta’adda su riƙe mana maƙogaro su riƙa sassafa mu da ƙasar nan ba.” Haka shugaban na Najeriya ba.
Yayin da ya ke bayar da umarni a gaggauta dukkan matakan tsaron da suka wajaba domin kauce wa sake afkuwar irin haka.
Ya ce a gaggauta dasa na’urorin da za su riƙa bibiyar zirga-zirgar jiragen ƙasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna da kuma tsakanin Legas zuwa Ibadan.
Ya kuma umarci Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta gaggauta gyarawa da kuma maido da sufurin jiragen ƙasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
Buhari ya kuma nanata umarnin sa na kakkaɓe dukkan ‘yan ta’adda da ɓatagari. Kuma kada a saurara wa duk wani mai riƙe da bindiga samfurin AK 47 ba bisa izni ba.
“Wannan hari ya yi muni sosai, kuma abin takaici ne. Ina miƙa ta’aziyya ga waɗanda suka rasa rayukan su da har yanzu ba a tantance yawan su ba. Ina kuma yi wa waɗanda aka ji wa rauni fatan samun waraka da gaggawa.” Inji Buhari.
Buhari ya jinjina wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin su na daƙile ‘yan bindigar tare da ceto da kuɓutar da sauran fasinjojin sa su ka yi.
Premium Times ta buga labarin yadda aka kai harin da kuma tabbatar da mutuwar mutum takwas.
Sai dai kuma a shafukan sadarwa ana ci gaba da nuna hotunan wasu da ake iƙirarin an kashe a harin.
Sannan kuma mutane da dama na watsa bayanan cewa an yi garkuwa da iyalan su ko wasu makusantan su.