Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa jami’an tsaron sun sanar wa gwamnatin jihar cewa mutum 34 ne ƴan bindiga suka kashe ciki har da sojoji biyu.
Kwamishina Aruwan ya ce hukumomin tsaro sun bada sunayen mutanen da suka mutu kamar haka,
– Angelina Aboi
– Godiya Iliya
– Peace Iliya
– Stephen Emmanuel
– Patrick Pius
– Gwamna Ishaya
– Philip Joseph
– Godwin Latong
– Aba Chawai
– Nancy Luka
– Sophia Luka
– Hosea James
– Daniel Sofa
– Geoffrey Ado
– Bala James
– Henry Dauda
– Augustine Iliya
– Irmiya Michael
– Murna Luka
– Monday Buki
– Reuben Kumai
– Zilien Gudak
– Anita Dauda Kawai
– Rifkatu Dauda Kawai
– Titi Bawa
– Jacob Yayock
– Samuel Ufui
– Silas Bulus
– Victor Ayuka
– Jummai Yunana
– Sunday Tachio
– Hope Luka
Sannan kuma akwai mutum 7 da suka samu rauni ana kula da su a asibiti yanzu haka.
– Ndau Abba
– Mani Luka
– Habila Sambo
– Ibrahim Daniel
– Julius Tachio
– Rose Sunday
– Sadunga Kamai
Akwai wata mace ɗaya mai suna Abigail Joshua data bace ba asan inda take ba.
Sakamakon binciken jami’an tsaro ya nuna cewa an kona gidaje akalla 200 da shaguna sama da 30. Baburan hawa 17 ne aka kirga duk an yi ragaraga da su.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya aika da sakon jaje ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma fatan Allah ya ba waɗanda suka ji rauni sauki cikin gaggawa.
A karshe gwamnan ya yi kira ga mutanen yankin da jiha baki ɗaya da su daina yanke hukunci da kansu, su rika zaman lafiya da juna sannan da hakuri da juna.
Discussion about this post