A wata takarda da mai taimakawa gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kan harkokin yada labarai Baffa Zailani da ya fitar, gwamnati ta nuna rashin jin dadnta kan kisan mutane da ‘yan bindiga sukayi a kananan hukumomin Bukkuyum da Maru.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka kashe mutane 24 inda a ciki akwai dakace da sarakunan gargajiya uku a kauyen Ganar Kiyawa.
Zailani ya ce gwamnati ta samu labari daga wajen jami’an tsaro kan yadda ‘yan bindigan suka kai hari a kananan hukumomin Maru da Bungudu duk a ranar Lahadin da ya gabata.
Ya ce ‘yan bindiga sun kai farmaki a wadannan kananan hukumomi a daidai jihar ta fara samun saukin hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan.
Duk da haka Matawalle ya tabbatar cewa gwamnati ba za ta ja da baya ba wajen ganin ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar.
Rundunar ‘Yan sanda
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu ya ce mutum 16 ne aka kashe ba mutum 24 ko 20 ba a kauyen Ganar Kiyawa.
Shehu ya tabbatar da haka a wani sakon tes da ya aika wa PREMIUM TIMES ranar Litini.
Ya tabbatar cewa rundunar ta aika da ma’aikatan ta domin Samar da tsaro a karamar hukumar.
Idan ba a manta ba a ranar Litini PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 24 inda a ciki akwai dagace daya, sarakunan gargajiya uku a kauyen Ganar Kiyawa ranar Lahadi da safe.
Mazauna kauyen sun ce mahara sun afka kauyen yayin da wasu mazauna ke dawowa daga gudun tsira da suka yi saboda harin ‘yan bindiga.
Sun Kuma tabbatar cewa ‘yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane daga kauyen sai dai basu da masaniyar yawan mutanen da aka tafi da su.