Jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta zargi tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje da yi wa shorin yin sulhu da ake yi zagon kasa.
Ana ƙoƙarin sasanta gwamnan jihar Inuwa Yahaya da sanata Goje da basu ga mai maciji.
Kakakin jami’iyyar Moses Kyari ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai acikin makon jiya.
A kwanan nan kwamitin sulhu na jam’iyyar APC wanda Abdullahi Adamu yake jagoranta ya gana da Yahaya da Goje, domin sasanta su.
Rikicin da wadannan shugabanin ke yi ya haifar da tashin hankali a jihar da rarrabuwar kai a jam’iyyar.
“APC na kira ga shugabannin jam’iyyar APC na kasa da su gaggauta daukar mataki da ja wa sanata Goje kunne tunda wuri kada lalacewar ta yi munin da ba za a iya shawo kanta ba.
“ Me ya sa sanata Goje ta hannun Manga zai ce sulhun da aka yi na Musulunci ne ba siyasa ba alhali rashin fahimtar juna tsakaninsa da Gwamna Yahaya ba shi da alaka da addini? Ya kamata Goje ya fito ya wanke kansa tunda wuri.” in ji APC.
Rashin jituwa tsakanin Goje da gwamna Inuwa Yahaya ya yi munin gaske da kullun maimakon a samu gyara abin lalacewa yake yi.
Idan ba a manta ba a dalilin haka jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagoranci gwamnan Ribas Nyesome Wike tare da tsoffin gwamnonin Ekiti, Fayose da Gombe Ibrahim Dankwambo suka yi masa ziyarar musamman da yi masa tayin ya dawo jam’iyyar PDP.