Kamfanin Sarrafa Simintin BUA ya bayyana cewa mutum uku da su ka mutu a sanadiyar gobarar da ta tashi a masana’antar Simintin BUA a Sokoto, ba ma’aikatan kamfanin ba ne, ‘yan ina-da-aiki ne.
Sanarwar da Sada Sulaiman, Daraktan Gudanarwa na BUA Cement ya aiko wa PREMIUM TIMES, ya ce waɗanda tsautsayin ya ritsa da su, su na aiki ne a ƙarƙashin wani mai aikin kula da gyare-gyare da lafiyar inji.
Premium Times ta buga labarin yadda wuta ta tashi a masana’antar a ranar Juma’a, har mutum uku su ka mutu, kuma wasu da dama su ka samu raunuka.
Sada Sulaiman ya ce wutar ta tashi a ɗakin da ake ajiye man ‘dizel’, kuma an yi ƙoƙari sosai an kashe wutar kafin ta kai ga shafar wasu ɓangarori na masana’antar.
“Lokacin da gobarar ta tashi an yi sauri an kira jami’an kashe gobara, su da ɓangaren kashe gobara na BUA, sun yi matuƙar ƙoƙari sun kashe wutar, sun kuma hana ta lasar wani ɓangare.
“Waɗanda su ka mutu ba ma’aikatan BUA ba ne, ‘yan ina-da-aiki ne da su ka zo aikin gyara tare da wani mai yi wa kamfanin gyare-gyare.
“Har yanzu ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba. Amma jami’an Kashe Gobara da na mu na kamfani su na ƙoƙarin binciko musabbabin tashin gobarar.
“Mu na miƙa ta’aziyyar waɗanda su ka mutu, kuma mu na kimanin waɗanda su ka ji ciwo.”