Jam’iyyar PDP ta yi wa APC gori tare da gwasale shugaban jam’iyyar da aka naɗa a wurin Gangamin Taron ranar 26 Ga Maris, a Abuja.
Gangamin dai bai tafi daidai yadda aka tsara shi ba, domin da dama sun nuna ɓacin rai dangane ya yadda ta kaya har aka fitar da shugabannin ba tare da an yi abin da su ke ganin cewa hakan ya fi dacewa ba.
Da yawa sun riƙa kukan cewa an cuce su, an naɗa masu ba abin da su ka so ba.
A nata raddin, PDP ta yi wa APC gwalo da shaguɓe cewa shugabancin sabon shugaban, Abdullahi Adamu haramtacce ne, kuma an damƙa jam’iyyar a hannun mai guntun kashin cin hanci, rashawa da wawurar kuɗaɗe a cikin wandon sa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran PDP, Debo Ologunagbe ya yi kaca-kaca da APC da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ya ce ta ɗaure gindin damƙa shugabancin APC ga kurar da bai kamata a ba ta ajiyar nama ba,
PDP ta ce ya kamata Abdullahi Adamu ya fito ya yi wa duniya bayanin inda Naira biliyan 15, wadda aka nema a hannun sa, shi da wasu jami’an gwamnatin Nasarawa su 19 da EFCC ta caje su da hutuma 149.
“Murnar da APC ke yi wai ta naɗa shugaba ko shugabanni, ba murna ba ce, shewar-dila ce. Su na murna ne a kan yadda cin hanci da rashawa su ka yi galaba a kan batun ci gaban ƙasa.
“Wannan taro ya nuna yadda gwamnatin Buhari ta ɗaure wa cin hanci da rashawa gindi ta hanyar yaudara aka naɗa shugabanni haramtattu a bisa jagorancin haramtacce, Abdullahi Adamu.
“Hakan da gwamnatin APC ta yi, ya nuna cewa ‘yan Najeriya za su ci gaba da rayuwar matsin tattalin arziki da ƙunci har tsawon shekara ɗaya kafin mulkin APC ya ƙare.”
Idan ba a manta ba dai PDP ta maka APC kotu a ranar jajibirin Gangamin Taron APC a Abuja.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda APC ta koma hannun ‘yan PDP, Abdullahi Adamu da Omisore.
Jam’iyyar APC ta amince da zaɓen Sanata Abdullahi Adamu sabon Shugaban Jam’iyya ba tare da jefa ƙuri’a ba.
An zaɓe shi ne bayan da sauran ‘yan takara su ka janye masa, a matsayin sa na wanda ya fi kwanta wa Shugaba Muhammadu Buhari a ran sa.
Adamu wanda tsohon ɗan PDP ne, ya shafe shekaru takwas ya na gwamna a Jihar Nasarawa ƙarƙashin PDP, tsakanin 1999 zuwa 2007.
Adamu ya shiga Majalisar Dattawa inda ya taka rawar neman Obasanjo ya zarce, yunƙurin da bai yi nasara ba.
Bayan saukar sa Gwamna, EFCC ta kama shi har ta nemi ya yi aman naira biliyan 15.
Lokacin da Adamu ke Gwamnan Nasarawa a matsayin ɗan PDP, shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF),
A Majalisar Dattwa ya zama Shugaban Ƙungiyar Majalisar Dattawa ‘Yan Arewa. Sai dai an tsige shi bayan da aka gano ya wawure wasu maƙudan kuɗaɗe.
Ya samu shiga wurin Shugaba Muhammadu Buhari tun a cikin 2015, inda a Majalisar Dattawa ya zama gogarman Shugaba Buhari, mai ragargazar Shugaban Majalisar Dattawa na lokacin, Sanata Bukola Saraki.
Omisore A ‘Next Level’: Yadda Ya Zama Mataimakin Shugaban APC Shekara Ɗaya Bayan Ya Shiga Jam’iyya Mai Mulki:
Iyiola Omisore ne aka zaɓa matsayin Mataimakin Shugaban APC, bayan ya doke tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ken Nnamani da Yakubu Dogara, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya.
Nnamani da Dogara duk tsoffin ‘yan PDP ne su ma. Omisore kuwa kafin ya koma PDP, ya yi Mataimakin Gwamna a Jihar Osun, ƙarƙashin jam’iyyar AD. Daga baya ya fice ya koma PDP.
Cikin Fabrairu 2021 ya canja sheƙa zuwa APC. Amma ana raɗe-raɗin cewa an saka masa ne da kujerar Matakimakin Shugaban APC saboda rawar da ya taka har APC ta kayar da PDP a zaɓen Gwamnan Osun cikin 2018, inda har Gboyega Oyetola ya zama Gwamna a 2018.
A zaɓen, PDP ke kan gaba, APC ta biyu sai Omisore na uku a ƙarƙashin SDP. INEC ta ce zaɓen bai kammalu ba, sai da aka sake zaɓe a wata rumfa.
Yayin da APC da PDP su ka fahimci cewa Omisore ba zai iya yin nasara ba, jam’iyyun biyu sun riƙa zawarcin sa domin ya umarci magoya bayan sa su zaɓi ‘yan takarar su.
Daga ƙarshe dai Omisore ya ce magoya bayan sa su zaɓi APC. Bayan Oyetola na APC ya yi nasara, shi kuma Omisore ya canja sheƙa ɗungurugum ya koma APC cikin 2021.
Sai dai kuma Adamu da Omisore za su hau kujera mai zafi, domin tun a farkon hawan su za ci gadon shari’a a kotu, wadda PDP ta kama APC ƙara, ta na neman a soke rajistar APC, a hana ta shiga zaɓen 2023, kuma a haramta taron gangamin da ya kai ga zaɓen su Abdullahi da Omisore a matsayin shugabannin APC.
Discussion about this post