Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kori jami’an Hukumar Kula da Filaye ta Jiha su huɗu, bayan kama su da laifin harƙalla da gada-gadar filaye.
Ganduje ya ce an kori mutanen huɗu, waɗanda dukkan su ma’aikatan Gwamnatin Jiha ne, saboda sun aikata zambar sayar da filayen jama’a, buga takardun haƙƙin mallakar filaye na jabu, bayar da takardun cancantar sanin bayanan filaye na bogi da kuma shirya gidogar bayanan gwamnati na ƙarya.
Sanarwar korar ta su na cikin wata takarda wadda Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano, Muhammad Garba ya sa wa hannu, mai ɗauke har da sunayen su da matakan albashin kowane daga cikin su.
Akwai Adulmunimu Usman Magami, Abdullahi Nuhu Idris, Audu Abba-Aliyu da kuma Baba Audu.
Kwamishina Garba ya ce an kore su bayan an kafa kwamitin binciken su, kuma kwamitin ya saurari koke-koken jama’a, tare da yin binciken da aka tabbatar sun aikata laifukan.
Ya ce korar ta su ta yi daidai da dokar aikin Gwamnati mai lamba 04406 ta tanadar.
Garba ya ce Gwamnatin Jihar Kano ba za ta taɓa amintar wasu ɓatagarin ma’aikata na karya dokokin tsarin aiki ba.
Daga ƙarshe ya ce ya na fatan wannan kora ta zama darasi ga sauran ma’aikatan jihar.