Bankin Duniya (World Bank) ya ce yawan masu fama da ƙuncin rayuwa, fatara da talauci a Najeriya zai kai mutum miliyan 95.1.
Bankin Duniya ya yi wannan mummunan albishir ga Najeriya a cikin wani rahoton da ya fitar mai suna Rahoton Bin Diggigin Talauci Da Fatara (Poverty Assessment Report).
Ya ce an ƙara samun adadin mutum miliyan 5 ne cikin 2022 sakamakon dukan jigatar da korona ta yi wa Najeriya da tattalin arzikin ƙasar.
Tun kafin sannan kuma dama Bankin Duniya ya ce shekarar 2020 ta je wa Najeriya a karkace, ta hanyar baddala mata lissafin tattalin arzikin ta.
Idan ba a manta ba, tsawon shekaru uku kenan Gwamnatin Buhari ke ta ƙara wa Barno dawakan ciwo tulin basusssuka daga waje da cikin gida, saboda ƙarancin kuɗaɗen da za a iya aiwatar da ayyukan cikin kasafin kuɗaɗe da su.
Tsadar rayuwa da ta haɗa da tsadar kayan masarufi, abinci, matsalar hawa da tsadar dala da rashin darajar naira, rufe kan iyakoki da aka yi da gagarimar matsalar tsaro sun hana da dama kasa tsallake siraɗin fatara da talauci a cikin 2021.
A shekarar 2018/2019 yawan matalauta su miliyan 82.9 ne a Najeriya. Zuwa shekarar 2020 kuma su ka kai mutum miliyan 85.2. sai kuma cikin 2022 inda har sun kai mutum miliyan 90. Nan da ƙarshen shekara kuwa za su iya kai mutum miliyan 95.1, inji Bankin Duniya.
Baya ga dalilan da Bankin Duniya ya bayyana a sama, ta ce rufe kan iyakoki, canjin yanayi na ambaliyar ruwa ko fari mai haddasa ƙarancin abinci da kuma uwa uba yawan haihuwar da ake yi, sun taimaka wajen rura wannan ƙaƙanikayi.
Bankin Duniya ya bada mafita cewa a ƙarfafa naira, a buɗe ƙofar samar da ayyukan da ba sai ƙarshen wata za a iya biyan lebura haƙƙin sa ba.
Bankin Duniya ya ce a 2018/2019 kashi 40.1 ne na yawan ‘yan Najeriya ke fama da talauci. Cikin 2020 kuma kashi 42. A cikin 2022 kuma sun ma kai kashi 42.6.