Gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike ya ragargaji tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Emmanuel Ortorm na jihar Benuwai cewa suna nema su tsinci dami ne a kale takarar shugaban kasa da suka fito a jam’iyyar PDP.
Wike ya bayyana haka a lokacin da ya ke bayyana ra’ayinsa na fitowa takarar shugabancin Najeriya a Makurdi babban birnin jihar Benuwai.
” Dukkan su ba su tsinana wa jam’iyyar PDP komai ba sai cika bakin da cewa ‘ ai da mune a ka kafa jam’iyyar PDP. Mune iyayen jam’iyyar amma ba za su iya nuna wani abu da suka yi wa jam’iyyar na azo a gani ba.
” Gaba dayan su sun arce daga jam’iyyar a 2015,suka kyale ta tana watangaririya. Nine kadai da rike jam’iyyar na ce bazan je ko ina ba ina nan a PDP sai naga abinda ya ture wa buzu naɗi.
” Don basu kunya, sai lokacin beman wani abu yayi sai su garzayo su ce suma suna son abu karkashin jam’iyyar. To basu isa ba domin kuwa za su sha kunya.
” Tun da kuka arce daga jam’iyyar PDP a 2015, wanda hakan yasa jam’iyyar ta faɗi a zaben shugaban kasa. Tunda sun gudu a lokaci su sani sun saida ƴancin su da duk wani iko da cika baki da suke yi na da su aka kafa jam’iyyar PDP.
Wike bai faɗi sunaye ba amma dai jefa ce yayi a kasuwa.