Gwamna Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya bayyana goyon bayan sa ga takardar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar wajen neman shugabancin Najeriya a ƙarƙashin PDP.
Fintiri ya bayyana haka ne a wurin taron ƙaddamar da neman fitowa takarar Atiku Abubakar a ƙarƙashin PDP, wanda aka ƙaddamar ranar Laraba a Abuja.
Fintiri wanda shi ma ɗan PDP ne, ya ce Atiku ne ya fi dukkan sauran ‘yan takarar kowace jam’iyya cancantar zama shugaban ƙasa, saboda ƙwarewa da gogewar sa da irin faɗi-tashin siyasa da mulkin ƙasa da ya daɗe ya na goyayya.
Daga nan Fintiri ya ce Jihar Adamawa za ta bai wa Atiku gagarimin goyon domin ganin cewa Atiku ya samu nasarar zama ɗan takarar PDP, kuma ya ci zaɓen 2023.
Fintiri ya nuna goyon bayan sa ga Atiku a yayin da rikici ya dabaibaye PDP a kan tsarin karɓa-karɓa.
Cikin shekarar da ta gabata ne PDP ta ce daga Arewa shugaban jam’iyyar su zai fito. A Arewar kuma an miƙa shugabanci ga Arewa ta Tsakiya, kamar yadda ita ma APC maj mulki ta yi. Daga nan ne kuma aka zaɓi Iyorchia Ayu daga Jihar Benuwai shugaban jam’iyya na PDP na ƙasa.
Mutane da yawa na tunanin PDP za ta miƙa takarar shugaban ƙasa ga mambobin ta na Kudu, kamar irin yadda ta ke tafiya tun daga 1999.
Kwamitin shirya taron PDP ya ce bai bayyana yankin da jam’iyya za ta bai wa kowane yanki takarar shugaban ƙasa.
Manyan PDP da su ka shiga takarar neman tsayar da su takara, sun haɗa Atiku Abubakar, Pius Anyim, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, Bukola Saraki, Dele Momudu da Sam Ohuabunwa.
Premium Times ta buga rahoton da ɗaya daga cikin masu nan tsayawa takara a PDP, Bukola Saraki, ya ce, ‘mu na ƙoƙarin fitar da ɗan takarar PDP a tsakanin mu, ba sai mun kai ga zaɓen fidda-gwani ba.’
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya bayar da tabbacin cewa masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP na ƙoƙarin cimma matsayar fitar da ɗan takarar da sauran za su mara masa baya, ba tare da an kai ga zaɓen fidda-gwani ba.
Saraki ya bayyana haka a Bauchi, lokacin da shi da Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto suka kai wa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ziyara.
Saraki ya ce shi da Tambuwal sun kai wa Bala ziyarar ce don neman amincewar sa a fitar da ɗan takarar da za su haɗu su mara wa baya, ko ma wane ne a cikin su.
Bala da Tambuwal su ma duk su na cikin masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP. Akwai na cikin huɗun su Atiku Abubakar, wanda shi ma ya fito takara.
“Mun haɗu mu uku mun tattauna batun zaɓen shugaban ƙasa a 2023. Mun yarda da cewa mafi muhimmanci dai shi ne haɗin kan ƙasa, haɗin kan PDP, ci gaban ƙasa da ci gaban jam’iyyar baki ɗaya sun fi muradin wani mutum ɗaya muhimmanci.
“Mun amince mu haɗa kai, mu goya wa mutum ɗaya daga cikin ɗan takarar da za mu fitar. Domin dai duk yadda ake je aka dawo, a ƙarshe dai ki zaɓe aka yi, to ɗan takara ɗaya ne zai yi nasara.
“Don haka gara tun daga yanzu mu fara shiri, wanda duk za mu amincewa mun tabbatar cewa ya cancanta.”
Daga nan kuma ya yi kira da magoya bayan PDP su ƙara tashi tsaye tsayin-daka wajen yi wa jam’iyya aiki tuƙuru.
Daga ya ce za su kai wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar irin wannan ziyara, domin shi ma a nemi amincewar a fitar da ɗan takarar PDP na zaɓen shugaban ƙasa ba tare da zaɓen-fidda-gwani ba.
Idan ba a manta ba, Premium Times Hausa ta buga labarin inda Tambuwal ya ce kada ‘yan Najeriya su zaɓi shugaban da ya kai ko ya haura shekaru 60 a duniya.