Ministan makamashi Abubakar Aliyu ya bayyana dalilan da ya sa ake samun matsanancin rashin wutan lantarki a kasar nan yanzu yana mai cewa karancin ruwa a tafkunan da ke juya injinan samar da wutan lantarkin ne yasa.
Tun daga farkon watan Faburairu ne aka fara samun matsanancin rashin wutan lanlarki a jihohi da yankunan kasarnan da dama.
Ministan wutan lantarki Abubakar Aliyu ya yi karin haske kan dalilin da ya sa ake samun matsalar rashin wutan lantarki a kasar nan.
Tun da aka shiga watan Fabrairu wasu bangaroriñ kasar nan ke fama da matsalar rashin wutan lantarki.
A taron da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Alhamis ministan ya ce ma’aikatar ta tsara hanyoyi guda uku domin shawo kan matsalolin rashin wutan lantarki da ake fama da shi.
“ Zan yi magana kan karin lodin da kuka gani a Abuja da sauran yankunan kasar nan sannan da raguwar ƙarfin ruwa a lokacin rani wanda a dalilin haka ya sa za a bukaci iskar gas domin rage lodin.
” A dalilin gyarar da ake yi a kusa da Odukpani ya sa aka samu raguwar wutar lantarki daga cibiyar samar da wutar lantarki ta NDPHC Calabar. Sannan Muna fama da wasu matsaloli a tashar iskar gas ta Okoloma wanda ke da alaƙa da tashar wutar lantarki na Afam VI.
“Za mu hada hannu da NNPC da sauran masu samar da iskar gas domin ganin an samar da wutan lantarki.
Aliyu ya ce gwamnati za ta bada kwangila wa kamfanonin samar da iskar gas domin ganin an samar da isashen gas din da za a bukata domin wadata kasa da wutan lantarki.
Ya ce gwamnati za ta dauki mataki akan duk kamfanin da ta baiwa kwangilan Kuma ta ki samar da iskar gas din akan lokaci.
“ Za a kammala gyara a tashar wutan lantarki dake Zunger, tashar wutan lantarki dake amfani da iska a Katsina, da Kashimbila Hydro sannan za mu hada hannu da ma’aikatar ruwa domin kawar da matsalolin da ake fama da su a Gurara. Za kuma mu warware matsalolin da suka hana manyan kan-grid dake amfani da hasken rana tashi a Najeriya.