Sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Matane ya bada wasu dalilai da ya sa matsalar hare-haren ƴan bindiga ya ki ci ya ki cinyewa a jihar.
Matane yayi wannan karin haske a wani shirin talabijin din ‘Channels’ ranar Alhamis.
Ya ce hare-haren ƴan bindiga ya zama babban sana’a inda har ‘yan bindigan na kiran ‘yan uwansu su zo su taimaka musu idan arangama da jami’an tsaro yayi tsanani.
Matane ya ce gwamnati ta gano cewa jami’an tsaron da take da su ba za su iya kare rayukan mutane ba saboda ƙaranci da suke da shi.
” Sau da yawa mutane za su kira su ce sun ga ‘yan bindiga amma kafin jami’an tsaro su kawo dauki ya kan ɗauki lokaci mai tsawon gaske har sai sun gama azazzalar mutane sun kama gaban su kafin jami’an tsaro su bayyana.
“Gwamnati ta ce jami’an tsaron na fama da matsaloli da suka hada karancin ma’aikata da kayan aiki.
Idan ba a manta ba shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin aikawa da dakarun sojin domin gamawa da ‘yan bint a jihar Neja amma har yanzu an ƙasa kawar da matsalar.
A makon da ya gabata ‘yan bindiga sun kashe DPO Muhammad Umar, ‘yan sanda biyu da ‘yan sa kai hudu a Neja.
Gwamnati ta ce mutum sama da 151,389 ne suka rasa gidajen su a dalilin hare-haren ‘yan bindiga a shekara biyu a jihar.
Mafi yawan mutanen an gano su daga kananan hukumomi 13 a jihar inda karamar humumar Rafi ce ta fi fama da hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Discussion about this post