Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i (SSANU) da Ƙungiyar Gamegarin Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (NASU), sun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin a cika masu alƙawarin su nan da 27 Ga Maris, ko kuma su kulle jami’o’in a rasa mai zuwa aiki baki ɗaya.
Cikin wata wasiƙa da SSANU da NASU su ka aika wa Ministan Ƙwadago Chris Ngige, sun zargi Gwamnatin Buhari da ƙin cika masu alƙawarin da ta ɗauka cikin Oktoba 2020 da wani da ta ɗauka duk a rubuce a cikin Fabrairu 2021.
A taron da su ka yi ranar Laraba, wanda bayan taron su ka aika wa ministan wasiƙa, mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren NASU, Peter Adeyemi da kuma Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, sun bayar ranar 27, ko dai gwamnati ta magance matsalolin su ko kuma ta fuskanci yajin aiki.
“Mun yi mamakin gano cewa tun makonni baya da muka bai wa Gwamnatin Tarayya, amma don wulaƙanci har yau ba ta yi wani abu ko da guda ɗaya ƙwaƙƙwara ba. Kai hatta ma ko sanar da cewa sun samu wasiƙar da mu ka aika, ba su yi ba.
“Mun aika da wasiƙa a ranar 1 Ga Maris, amma babu abin da aka yi.
Cikin makon jiya ne dai ASUU ta ƙara maƙonni 8 kafin ta sake waiwayen Gwamnatin Tarayya, ta ce ‘gwamnatin maƙaryata’ ce.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bayyana ci gaba da yajin aiki har ƙarin tsawon watanni biyu nan gaba, kafin ta sake waiwayar Gwamnatin Tarayya.
Shugabannin ASUU sun kwana taro a Hedikwatar su da ke Jami’ar Abuja, wanda su ka fara tun daga ranar Lahadi, har zuwa wayewar garin yau Litinin.
Wata majiya daga cikin mahalarta taron ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa tabbas sun kwana taro, kuma sun yanke shawarar cewa za su ci gaba da yajin aiki, tunda gwamnatin tarayya ta ɗauke su sakarkaru.
Majiyar wadda ta ce kada a ambaci sunan ta, ta ce za su ci gaba da jayin aiki har sai sun nuna wa gwamnatin tarayya cewa lallai ta watsar da ilmi a ƙasar nan, ta bar shi ya na neman lalacewa.
Majiyar ta ce yanzu haka ana nan ana rubuta takardar bayan taro wadda za a raba wa manema labarai.
Malaman inji majiyar sun zargi Gwamnatin Tarayya da rashin cika alƙawari, yin baki biyu da kuma zumbuɗa ƙarya.
A baya dai bayan gwamnati ta sha yi wa ASUU alƙawari, kwanan baya Gwamnatin Tarayya ta fito ta ce ba ta da kuɗaɗen da za ta iya biyan buƙatun malaman jami’o’i.
Dama kuma watanni biyu baya ASUU ta ce idan sun sake tafiya yajin aiki, to a tuhumi Buhari, gwamantin sa ce ta kasa cika masu alƙawari ko da guda ɗaya.