Ministan Sufurin Rotimi Amaechi ya bayyana cewa daga yanzu jiragen saman yaki ne za su dinga yi wa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna rakiya idan aka gama gyaran ɓarnar da ƴan bindiga suka yi wa layin dogon da jirgin kasan.
Minista Amaechi ne ya bayyana haka ranar Laraba a ziyarar gani wa Ido abin da ya faru bayan harin da ƴan ta’adda suka kai wa jirgin a ranar Litinin.
Amaechi ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin dake kwance a Asibitin 44 na Sojoji a Kaduna, sannan kuma ya gana da Hafsan Sojojin Sama Air Marshal IO Amao da kuma Gwamna Nasir El-Rufai.
“Na faɗa wa hafsan sojan sama cewa idan muka gama gyaran layin dogo, jirgin zai ci gaba da aiki bisa rakiyar tsaro ta sama daga sojan sama har sai an saka kayayyakin tsaro daga nesa kamar yadda shugaban ƙasa ya ba da umarni,”
Idan ba a manta ba ko a jawabin da yayi a lokacin da ya kai ziyara inda harin ya auku, Amaechi ya ce da za a iya dakile aukuwar wannan hari idan da an bi shawarar da ya baiwa gwamnati na a saka na’urorin hangen nesa da gano bam a layin dogo da aka yi masa kunnen uwar shegu.
Amaechi haɗari ne da za a iya kauce wa amma kuma aka barshi ya auku.
Akalla mutum 8 ne suka riga mu gidan gaskiya a wannan hari inda wasu 27 suka samu rauni.
Maharan sun sace mutane da dama wanda har yanzu ba a san inda suke ba.