Ɗan wasan Real Madrid Karim Benzama ya kafa tarihi a duniyar ƙwallo, yayin da ya ci ƙwallaye uku a cikin mintin a 16, a wasan da Madrid ta yi da SPG ta Faransa, ranar Talata.
Benzama ya ci ƙwallayen ne waɗanda suka sa a yanzu dai a tarihin gasar Champions League shi ne mai yawan shekarun da ya taɓa cin ƙwallaye har uku a rana ɗaya. A yanzu shekarun sa 34 da kwanaki 102.
Wannan ƙwallaye da ya sharara wa PSG Cikin mintina 16, sun kuma kai shi ga zama ɗan wasa na uku mafi ci wa Madrid ƙwallaye.
Benzama ya sha suka a shekarun baya, musamman yadda Cristiano ya danne shi ya fi shi cin ƙwallaye.
Bayan Ronaldo ya bar Madrid zuwa Juventus, Benzama ya zage damtse, ya riƙa zama abin dogaro wajen cin ƙwalloye sosai, har ma ake ganin ya na a sahun farko na mashahuran yanzu.
Real Madrid dai ta fita kunyar wannan wasa, wanda idan da PSG ta fitar da ita, za ta karya mata duk wani kafin sake yin wani kataɓus a gasannin da ke gaban ta.
Baya ga Ronaldo, Alfred Di Stefino ne kaɗai su ka kai ko suka wuce Benzama ci wa Madrid ƙwallaye.
Halin Benzama ya sha bamban da na Ronaldo. Benzama bai taɓa neman a yi masa ƙarin albashi ko kuɗin kwantaragin sa ba. Kuma bai taɓa neman a ƙara masa wa’adin zama Real Madrid ba.
A shekarun baya Benzama ya sha tsangwama, musamman har ƙin tafiya da shi gasar cin kofin duniya an yi a 2018, saboda ƙorafin ba ya iya cin ƙwallaye.
Amma yanzu duniyar ƙwallo ta ƙara shaida cewa Benzama na nan gagau, bai yi mutuwar-tsaye ba. Ko inda babu ruwa aka shuka shi, zai fito kuma ya yi yabanya.
Wasan Kece Raini A Ranar Fita Kunya:
Real Madrid ta shiga fili domin karawa ta biyu, bayan SPG ta doke ta da ci ɗaya mai ban haushi a Paris. Kylian Mpape ne ya yi wa Madrid cin wulaƙanci, kuma a wasan ranar Laraba da dare a Madrid, shi ne dai ya fara jefa wa Madrid ƙwallo, kafin Benzama ya fusata ya jefa ƙwallaye uku a ragar PSG a cikin mintina 16.
Madrid ta shiga fili ba tare da mashahuran ‘yan wasan ta biyu ba, Ferlan Mendy da Casemiro waɗanda katin gargaɗin da aka ba su ba wasan baya ya haramta masu buga wasan na jiya da dare.
PSG ta zo da gwanayen da take taƙama da su, har da Leonel Messi, tsohon ɗan wasan Barcelona, da kuma takwaran sa Neymar Jr. Haka kuma dama ƙungiyar cike ta ke da tsoffin ‘yan wasan Real Madrid, duk da dai wasun su ba su buga ba.
Har aka koma hutun rabin lokaci PSG ke kan gaba da ƙwallaye 2 da ta ci ɗaya a Paris ɗaya kuma a filin Santiago Bernabeu na Madrid.
Bayan an dawo rabin lokaci ne wasa ya sauya, Madrid ta nuna masu ruwa ba sa’ar kwando ba ne.
Shekaru bakwai kenan a jere Madrid na kai ga matakin ‘kwata fenal’ a gasar Champions League.