Daga Daura har Delta. Daga Dankama har Dogon Daji. Daga Enugu har Pataskum. Daga Legas har Kwatarkwashi, yanzu a Najeriya duk wanda ya ce maka ya na shan fetur a daidai yadda ya ke so kuma a lokacin da ya ke so a kan ƙa’ida, to bai faɗa maka gaskiya ba.
Sayen fetur a wahalce, kamar yadda samun hasken lantarki shi ma a wahalce. Hakan kuma duk na faruwa ne a daidai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ke ƙoƙarin cika shekaru bakwai kan mulki.
Ana fama da wannan matsanancin ƙarancin fetur ne alhali kuma Shugaba Muhammadu Buhari ne Ministan Fetur na Najeriya.
Alƙawarin da Buhari ya yi na gyara matatun mai na ƙasar nan huɗu idan ya hau mulki, ya zama tatsuniya kenan.
Ana fama da matsananciyar wahalar fetur wadda shekaru da dama ba yi kamar ta ko kwatankwacin ta ba. Cikin wannan makon ne kuma PREMIUM TIMES Hausa ta yi bajekolin mutane huɗu, “waɗanda su ka jefa Najeriya a hannun ‘yan bumburutu.”
Matsalar fetur da tsadar gas ta gurgunta ayyukan da hanyoyin neman kuɗi ko neman abincin miliyoyin ‘yan Najeriya. Waɗanda sun dogara da fetur da gas wajen aikin su, sun fi kowa shiga jangwangwama a wannan yanayi da ake ciki, wanda kuma ba a san ranar fita daga ciki ba.
Ita wannan masifar matsalar fetur, tamkar mutuwa ta ke. Domin ko a ina ka ke sai ta shafe ka. Yayin da ta addabi masu motocin kan su, haka ta addabi direbobi da fasinjoji. A sama, masu kamfanonin jiragen sama da fasinjojin jiragen sama na fama da jidalin ƙaranci da tsadar man jirgi, wanda ya haifar da tsadar tikitin jiragen sama.
Ƙuncin Rayuwar Tattalin Arziki Da Masifar Matsalar Tsaro:
A waɗannan ɓangarori biyu ne Shugaba Buhari ya ce zai fi maida hankali kafin a zaɓe shi da bayan an zaɓe shi.
Sai dai kuma maimakon ‘yan Najeriya su samu sauƙi, sai dai cewa “ba sauƙi, wai ciwon mahaukaciya.”
A lokacin da Buhari ke kamfen cikin 2014 a filin wasa na Fatakwal, ya shaida cewa “idan na zama shugaban ƙasa zan zaɓo ƙwararru domin ya naɗa su a manyan muƙamai na gwamnati, domin su gyara rigar mutuncin tattalin arzikin Najeriya, wadda ta ratattake.
Bayan Buhari ya hau mulki a ranar 29 Ga Mayu, 2015, maimakon ya gaggauta kafa gwamnatin sa, sai da ya shafe watanni shida sannan ya naɗa ministoci. Waɗanda ya naɗa ɗin ma, ta wani mawaƙi, daga yawan su akwai “gurgure da mazallaƙo, shi da turkai da rabsago, ɗantanƙe da aholaki.”
Yayin da a shekarar 2012 da 2013 Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai (NBS) ta ce mutanen da fatara da talauci su ka yi wa katutu a ƙasar nan sun kai mutum miliyan 83, wani lissafi a 2022 ya ce adadin zai kai mutum miliyan 90. Haka dai wani masani mai suna Banji Olatoye ya bayyana.
Haka ake ta gaganiya, abinci tsada, fetur tsada kuma ga wahalar nema a samu, hatta Abuja Babban Birnin Tarayya lamarin ya yi muni matuƙa.
Karin halin ƙuncin kuma shi ne a daidai wannan lokaci ake fama da yawan ciwo bashi da gwamnatin Buhari ke yi. Ta kai ko a bakin kura gwamnatin Buhari ta ka kuɗi, sai ta jaraba karɓo su bashi.
Banda wannan kuma a ciki wannan halin ne kuma darajar naira ke ci gaba da faɗuwa ƙasa warwas, ta inda a kasuwar ‘yan canji har ta kai naira 575.
Matasan Najeriya Kaicon Ku:
Rahoton Rashin Aiki da NBS ta buga na baya-bayan nan ya nuna matasan Najeriya daga ‘yan shekaru 15 zuwa 34, akwai aƙalla miliyan 21.72 waɗanda ba su aikin fari ballantana na baƙi.
Rahoton Disamba 2020 ya nuna kashi 33.3 na majiya ƙarfin Najeriya ba su da aiki.
Wannan gagarimar matsala ce Olatoye ya kira da “bam ɗin da ke jiran a taɓa shi kaɗan ya fashe daram!”
Discussion about this post