Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo, inda ta lallasa ata da ci 4-0.
Wasan wanda aka buga shi a filin wasa na Beneu Bau dake babban birnin Madrid ya samu halarta dubban magoya bayan kungiyoyin biyu.
Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci Barcelona ta ɗirka kwallaye biyu a ragar Madrid.
Da ya ke sun saba cewa ai su idan suka dawo hutun rabin lokaci ne suke maida martani sai gashi a wannan karon ba su samu daman yin hakan ba.
Bayan an dawo hutun rabin lokaci sai Barcelona ta nuna wa Madrid cewa da gaske take.
Kafin a karkare wasa, Barcelona ta ta sake narka wa Madrid kwallaye biyu bayan ɓari da ta yi da dama.
Discussion about this post