Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa daga yanzu Atiku Abubakar yake yi ba ‘Bukola saraki’ da kowa ya sanshi da shi ba.
Sanata Dino ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar nuna goyon baya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
A bidiyon da ya karade shafukan yanar gizo, an nuno Dino ya na wasa Atiku Abubakar yana ma cewa ” Ko da aka ganni na taho nan wasu abokai na sun tambaye ni cewa yayakuma aka ga na garzayo wurin Atiku, maimakon wanda aka sanni da shi muna tare ‘Saraki’ sai na ce musu ai tuni na kama gaba na.
” Na daina bin ‘yan takaran dake lalube cikin duhu, na koma ga wandanda suna gani gadagau sun san kabli da ba adin siyasa da gogayya a fagen takara.
Sanata Dino yayi kaurin suna a majalisar da ta shude inda shi ne karaen farautar shugaban majalisan Bukola Saraki.Kamar yadda wasu ke gani a wancan lokacin.
Ko da Saraki ya bayyana ra’ayin sa na fitowa takarar shugaban kasa, mutane da dama sun ce ba sai Dino ya bayyana inda alkiblar sa ya ke sai kuma yanzu aka ga akasi.
Discussion about this post