Yayin da ‘yan Najeriya ke cikin halin ƙuncin rashin wutar lantarki, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa a cikin mulkin Buhari bankin ya kashe naira tiriliyan 1.3 wajen ƙoƙarin ganin an bunƙasa kuma an inganta wutar lantarki a faɗin ƙasar nan.
Gwamnan CBN Dodwin Emefiele ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, a ranar Litinin.
Wannan bayani na sa ya zo ne kwana kaɗan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Najeriya haƙuri saboda gagarimar matsalar wuta da ake fama da ita a ƙasar nan, tun a farkon watan Fabrairu.
Emefiele ya yi wannan sanarwa a ranar da Buhari ya kira Misitan Makamashi Abubakar Aliyu domin jin halin da ake ciki dangane da matsalar wutar lantarki.
A yanzu haka tashoshin samar da wuta 14 duk sun durƙushe, lamarin da ya jefa Najeriya cikin duhu.
Sai dai kuma abin mamaki shi ne irin adadin maƙudan kuɗaɗen da CBN ya kashe a cikin shekaru biyar na mulkin Buhari, zai ba jama’a da dama mamaki.
Emefiele ya ce CBN ta kashe Naira tiriliyan 1.3 ta fannoni daban-daban don inganta wutar lantarki a Najeriya, a cikin shekaru biyar da suka gabata.
“Mun kashe Naira Tiriliyan 1.3 cikin shekaru biyar, ko dai ta hanyar sayen manyan janareto na wuta, raba kuɗaɗe ga kamfanonin saida wuta, ‘Discos’, ko ta dalilin sayo kayan ingina da kayan gyara, ko sayen mita, ko kuma ƙarin kuɗaɗe ga kamfanonin samar da wuta.
Alƙawarin Gyara Matsalar Wuta: Tunatarwar SERAP Ga Buhari Kan Kasa Cika Alƙawari:
‘Ka cika alƙawarin da ka ɗauka ranar rantsar da kai, ka ce za ka binciki yadda kuɗaɗen gyaran wuta su ka salwanta, amma shiru’ -SERAP ga Buhari
Ƙungiyar SERAP ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari cewa ya sa Ministan Shari’a Abubakar Malami da EFCC da ICPC su binciki masu hannu wajen kashe aƙalla Naira Tiriliyan 11 a ɓangaren gyaran wutar lantarki, tun daga 1999 har zuwa yau.
SERAP ta ce ba zai yiwu ƙasa kamar Najeriya ta riƙa kasancewa cikin duhu ba, amma a duk shekara wasu na danne biliyoyin nairorin da ake warewa da sunan gyaran matsalar wutar lantarki.
Wannan kira na SERAP ya zo ne daidai lokacin da Najeriya ke cikin wata gagarimar matsalar wutar lantarki, inda yawan wanda ake samu bai wuce wats 2200 ba.
Bugu da ƙari kuma tashoshin samar da hasken lantarki 14 a ƙasar nan duk sun durƙushe.
SERAP ta ce daga 1999 zuwa yau, an ragargaje zai kai naira tiriliyan 11, wuta ba ta gyaru ba, sannan babu kuɗaɗen babu alamar su, an yi biyu-babu kenan.
Kan haka ne SERAP ta ce a gaggauta yin bincike, a kamo, a gurfanar kuma a ɗaure duk wanda aka samu da laifin karkatar da kuɗaɗen aikin gyaran wuta ko wane ne. Sannan kuma a taka cikin sa sai ya amayar da kuɗaɗen da ya karkatar.
Wannan wasiƙa dai SERAP ta aika wa Buhari ita a ranar 19 Ga Maris, mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare.
“An shafe shekaru masu ‘yawa ana yi mana ‘yar-burum-burum kan aikin gyaran wutar lantarki a ƙasar nan.
“SERAP na runatar da Buhari cewa sai ka cika alƙawarin da ka ɗauka a ranar rantsar da kai, 29 Ga Mayu, 2015, sannan wuta za ta gyaru.
Matsalar Lantarki: Alƙawarin Buhari A Ranar Rantsar Da Shi:
“Babban abin kunya ne a ce kamar Najeriya ƙasa mai sama da mutum miliyan 180 amma ba su iya samun wutar da ta wuce miga wats 4000. Ba za
mu taɓa barin haka ya ci gaba ba.” Inji Buhari a cikin jawabin sa a 2015.
Sannan kuma SERAP ta nemi Buhari ya bi umarnin kotu wanda Mai Shari’a Austine Chuke Obiozor ya umarci Gwamnantin Tarayya tun a cikin 2019 cewa ta fallasa sunayen waɗanda su ka ci kuɗaɗen gyaran wutar lantarki, sunayen kamfanoni da adadin kuɗin da kowa ya salwantar.
Discussion about this post