Magoya bayan kwamishinan kananan hukumomin jihar Kano Murtala Sule Garo da na Kabiru Rurum sun kaure da fada a wajen kaddamar da sabbin shugabannin APC da aka yi a filin Taro na Rano a karshen makon jiya.
Rikici ya barke ne a lokacin da magohya bayan jigajigan ‘yan siyasa a lokacin da suka hadu a wajen taron.
Baya ga mutum hudu da aka kashe anji wa mutane da yawa rauni a wannan arangama.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya raba motoci ga ‘yan siyasa da bayan rantsar da shugabannin jam’iyyar a garin Rano.
Dan uwan daya daga cikin wanda aka kashe Abba Abdullahi, Hamisu Abdullahi da aka fi kira da AGA, wanda kuma mahauci ne ya ce a wannan rana dan wuansa ya ki zuwa kasuwa aikin nama ya nausa can wurin taro inda a nan ne aka kashe shi.
Abba ya ce an yi wa Aga mummunar sara ne a wuya ashe kuma ya zo da karewar kwana. Ya rasu ya bar matarsa daya da ‘yar sa daya.
Haka shima, Dan-Mamadu Kaura daga Garo ya rasa ran sa a wannan rikici. Ya rasu a wani asibitia cikin Kano.
Bayan su akwai wasu mutum biyu da suka rasu a sanadiyyar rikicin a wannan wurin taro.