Sabon Gwamnan Jihar Anambra, wanda aka rantsar cikin makon da ya gabata, Charles Soludo ya ce ya ci gadon naira miliyan 300 kaɗai daga gwamnatin Obiano, wanda ya sauka makon jiya.
Da ya ke bayani a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin safe na Gidan Talabijin na Arise a ranar Laraba, Soludo ya ce an bar kuɗi cikin cokalin da ba su wuce naira miliyan 300 zuwa 400 ba, amma kuma tulin bashin da gwamnatin da ta sauka ta bari ya kai Naira biliyan 109.
Ya ce amma wannan ba zai sare masa guyawu ba, zai yi aiki tuƙuru domin bunƙasa jihar Anambra, duk kuwa da cewa asusun jihar babu komai a ciki.
“Kuɗin da mu ka taras ba su wuce Naira miliyan 300 zuwa miliyan 400 ba. Sai kuma tulin bashin da ya zuwa ranar 31 Ga Disamba, 2021 bashin da ake bin Anambra ya kai Naira biliyan 109.” Inji Soludo.
Daga nan ya ce zai bunƙasa jihar ta hanyar maida hankali kan amfani da kayan cikin gida, maimakon na ƙasashen waje.
Ya ce bai ga dalilin da zai sa a riƙa fifita kayan waje ba, alhali ga na gida.
“Yanzu a ce mutum miliyan 215 na Najeriya duk da yadin da ake yi a nan gida su ke ɗunka sutura, ai da an samu ci gaba sosai. Kuma miliyoyin mutane za su samu aikin yi.”
Premium Times ta buga labarin yadda EFCC ta damƙe Willie Obiano yayin da ya ke shirin tserewa Amurka, bayan an gaggaura wa matar sa mari a wurin da ya damƙa wa Soludo mulki Jihar Anambra.
Jami’an EFCC sun ɗauki tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano cancak daga ofishin su na Shiyyar Legas zuwa Hedikwatar EFCC ta Abuja domin ci gaba da sharara masa tambayoyin salwantar maƙudan kuɗaɗe a lokacin mulkin sa.
Obiano zai sha tambayoyi bayan kuma an sharara wa matar da Misis Obiano mari a gaban jama’a, yayin da su ke miƙa mulki ga sabon Gwamnan Anambra, Charles Soludo.
EFCC ta kama Obiano a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Abuja, sa’o’i kaɗan bayan ya miƙa mulki a Enugu.
Ya garzaya Legas ne da nufin hawa jirgin sama zuwa Jihar Houston a Amurka, inda jirgi ke jiran sa.
Wannan rana ta zama baƙar rana ga Obiano, wanda a gaban sa kuma a gaban dubban jama’a, Bianca Ojukwu ta gaggaura wa matar sa mari wurin miƙa mulki.
Majiyar EFCC ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an damƙe Obiano wajen ƙarfe 8:30 na dare a ranar Laraba, kuma washegari Alhamis aka ɗauko shi a jirgi zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.
Har yanzu dai ba a san takamaiman ko naira biliyan nawa EFCC ke ƙoƙarin ganin Obiano ya amayas ba.
Sai dai kuma idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labari ƙarshen 2021 cewa Hukumar EFCC ta rubuta wa Hukumar Shige da Fice Wasiƙa a ranar 15 Ga Nuwamba cewa su sa ido kan Obiano duk inda zai fita daga ƙasar nan. Su kula da ranar da zai fita ko ranar dawowar sa.
EFCC ta kama shi sa’o’i kaɗan bayan ya rasa rigar sulken kariya a lokacin ya na gwamna, rigar da ke hana duk irin ɓarnar da gwamna ya yi, ya fi ƙarfin kamu, sai dai a jira bayan saukar sa.