Idan ba a manta ba, Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da harin da aka kai wa jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ranar litinin.
A sanarwar da ya fitar ranar Litinin da dare ya ce bayan samun rahotanni cewa ƴan ta’adda sun tada bam a layin jirgin da ya sa dole jirgin ya tsaya.
Wani da ke cikin jirgin ya bayyana cewa an yi ɓarin wuta tsakanin ƴan sandan dake cikin jirgin da ƴan ta’addan na tsawon wani lokaci kafin sojoji soka lawo ɗauki.
Wannan ba shine karon farko ba da ƴan ta’adda ke kokarin kai farmaki ga jirgin Abuja zuwa Kaduna.
Jirgin kasa dake jigila daga Kaduna zuwa Abuja ya zama mafita ga matafiya da dama saboda ayyukan ƴan ta’adda da suka addabi matafiya a titin Abuja – Kaduna.
Mutane da dama sun ji rauni amma an garzaya da su asibiti. Sannankuma duka fasinjojin da ke cikin jirgin sun tsira babu wanda aka sace.
Sai dai kuma Aruwan ya ce za a duba sunayen matafiyan dake cikin jirgin domin sanin halin da kowa ke ciki da kuma sanin ko kowa ya tsira.
Zuwa safiyar Talata din nan, Aruwan yace an kammal kwashe duka matafiyan da harin ya ritsa da su sannan kuma gwamnati za ta ci gaba da aiki da hukumar jiragen kasa domin samun sunayen mutanen da suka shiga wannan jirgi.
Attajirai da masu fadi a ji, duk sun koma ta jirgin lasa suke bi zuwa Kaduna ko Abuja.
Wannan hari da ake kai wa jirgin zai daɗa tsorata matafiya da suke ganin bin jirgin kasa shine mafita daga afkawa ƴan ta’adda da suka addabi hanyoyin mota a yankin jihar.