Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka USCDA ta samar da maganin cutar kanjamau wa mutum miliyan 1.7 a Najeriya.
Jami’ar hukumar Mary Boyd ta sanar da haka ranar Laraba a Abuja a taron tsare-tsaren taron inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya da za a yi mako mai zuwa a Abuja.
Mary ta ce USCDA ya taimaka wajen inganta yi wa mutane allurar rigakafi cututtuka musamman korona, zazzabin cizon sauro da dai sauran su.
“Gwamnatin Amurka ta tallafa wa gwamnatin Najeriya wajen dakile yaduwar cututtuka ta hanyar inganta yi wa mutane allurar rigakafi yanzu Amurka za ta kara tallafa wa Najeriya wajen ganin ta inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin samar da ingantaccen kiwon lafiya wa mutane a kasar.
Ta ce bullowar cutar korona ya taimaka wa kasashen duniya wajen inganta fannin kiwon lafiyar su sannan a Najeriya ya taimaka wajen bayyana aiyukkan da ya kamata cibiyoyin kiwon lafiya na yi.
Daga nan Mary ta yabawa kokarin da gwamnati, ma’aikatar lafiya, NPHCDA da NCDC suka yi wajen yaki da cutar korona.
“Ina Kuma so na mika godiya ta ga gwamnatin Najeriya bisa kokarin shirya taron inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya domin samar da kiwon lafiya wa mutane.
Za a fara taron inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a Abuja daga ranar 24 zuwa 25 ga Maris.
Taron zai maida hankali wajen tattauna matsalolin dake gurguntar da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin hada hannu da kowace fanni a kasan domin kawar da su.
Discussion about this post