Bayan alƙawurran da Gwamnatin Tarayya ta sha yi wa Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta biya buƙatun su domin su daina yajin aiki, a yau kuma gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da kuɗaɗen da za ta iya biya wa malaman jami’o’i buƙatun da suke nema ɗin.
Ministan Ƙwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin da Gidan Talabijin na Channels ke hira da shi a ranar Alhamis.
Kafin tafiyar ASUU yajin aiki makonni biyu da suka gabata, ƙungiyar ta ce duk da alwashi da alƙawarin da gwamnatin tarayya ta ɗauka bayan masu shiga tsakani, har da shugabannin ɓangarorin addinai sun sa baki, har yau gwamnatin ba ta cika alkawari ko ɗaya ba.
Idan ba a manta ba kuma, bayan an shiga tsakani a cikin watan Janairu, ASUU ta ce “idan malaman jami’o’i su ka sake tafiya yajin aiki, to a tuhumi Buhari, shi ne bai cika alƙawari ba.
Babba daga cikin alƙawarin da har yau aka kasa cika wa ASUU shi ne wanda Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a rubuce (MOU) cewa za ta aiwatar (MOA), kuma ta sa hannu tun a cikin 2009.
ASUU ta soki gwamnati da yi masu wasa da hankali wajen ƙin biyan alawus, sai kuma biyan wani alawus ɗin cikin cokali, wanda kamata ya yi a biya su cikin bokiti.
ASUU ta yi ƙemadagas wajen ƙin yarda a ci gaba da biyan su albashi a tsarin IPPS na ƙeƙe-da-ƙeƙe, inda suka ce kamata ya yi a riƙa biyan su a ƙarƙashin tsarin biyan albashi na UTAS, wanda gwamnati ta yi watsi da shi.
Yayin da ASUU ta ce ba za su koma aiki na, shi kuma Minista Ngige ya ce ana nan ana tattaunawa domin a cimma matsaya, su amince su janye yajin aikin.
“Jama’a su lura fa gwamnatin tarayya ta ɗauko hanyar cika alƙawarin da ta ɗauka, domin har ya ramto Naira biliyan 200 daga Asusun Hukumar TETFund ta bai wa malaman jami’o’i. Kuma wannan biyan kuɗaɗen ariyas ne tun daga 2016 har zuwa cikin wannan mulki na mu.” Inji Ngige.
“Alƙawarin da ake ja-in-ja a kan sa yanzu, tun na cikin 2016 zuwa 2017. To a gaskiya ba mu da kuɗin a yanzu, amma dai za mu san yadda za mu bubbuga mu nemo kuɗin domin mu farfaɗo da jami’o’in da farfaɗo da kayan aiki da gine-ginen da ke da buƙatar ingantawa.”
Yadda Ta Kaya Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Buhari, Kafin A Sanarwar ‘Babu Kuɗi’:
ASUU Ta Ce Har Yau Gwamnatin Tarayya Ba Ta Cika Ko Da Alƙawari Ɗaya Tak Ba:
Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya sake ɗaukar alƙawarin cewa yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta fara tsawon mako guda kenan, zai kawo ƙarshe kafin ƙarshen wannan wata na Fabrairu.
Sai dai kuma ASUU ta yi masa kunnen-ƙashi, inda ta ce za su ci gaba da yajin aiki, tunda dai har yau ɗin nan Gwamnantin Tarayya ko alƙawari ɗaya gyan-gyan ba ta cika masu ba.
Yayin da Ngige ke bayani a ranar Talata, yayin da aka koma kan teburin tattaunawa, ya ce gwamnatin tarayya ta yi mamakin yadda ASUU ta sake rankayawa yajin aiki, duk kuwa da shiga tsakani da manyan masu ruwa da tsaki a ƙasar nan suka yi, cikin su kuwa har da manyan shugabannin addinai a ƙarƙashin ƙungiyar NIREC.
Duk da haka dai Minista Ngige ya shaida wa wakilan ASSU cewa, “ina tabbatar maku wannan taro da muka yi zai haifi ɗa mai ido.”