Gwamnatin jihar Kaduna ta gargaɗi mutanen garin Kaduna da su yi takatsantsan da kuma sa ido a duk lokacin da aka fita gida ko kuma aka wulƙawar bakon fuskar da ba a sanshi ba yana galantoyi a unguwa.
Kwamishinan tsaron jihar ya bayyana cewa an samu bayanai daga jami’an tsaro cewa akwai yiwuwar ƴan ta’adda, wato ƴan bindiga sun daddasa bamabamai a wuraren da jama’a ke taruwa a faɗin jihar.
Irin waɗannan wurare sun haɗa da makarantu, tituna, kasuwanni, wuraren shakatawa, Masallatai da Coci Coci, tashoshin motoci da dai sauransu.
Gwamnati ta hori mutane su rika nesa-nesa idan suka ga ƙunshin wani abu an ajiyeshi da basu san ko menene ba. Sannan kuma idan suka ankare da bakon fuska a ciki su su gaggauta sanar da jami’an tsaro ta hanyar kiran waɗannan lambobi kamar haka, 09034000060 da 08170189999.
Haka kuma sanarwar ta gargadi masu fasa dutse su rika killace kayan aikin su domin kada ɓatagari su iya kaiwa garesu.
Fashewar bam a Kabala West
Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna, Mohammed Jalige ranar Litinin ya tabbatar da fashewar bam a unguwar Kabala west ranar Litinin.
Bam ya fashe a unguwar Kabala ranar Lahadi sai da babu wanda ya ji rauni ko ya rasa ransa.
Jalige ya ce bam ɗaya n ya fashe ne a wani gida a lokacin da babu kowa a gidan, sannan ya kara da cewa rundunar na ci gaba da bincike akai domin sanin ainihin abinda ya auku a wannan gida da yadda aka yi bam ya tashi a gidan.
Discussion about this post