Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya ce da tun farko Kungiyar Ƙasashen Taron Dangin NATO sun ji gargaɗin wasu shugabannin cikin ƙungiyar, da Rasha ba ta fusata har ta hau kan Ukraniya da yaƙi ba.
“Tsawon shekaru da dama wasu daga cikin shugabannin ƙasashen cikin ƙungiyar NATO sun sha yin gargaɗin cewa ƙara yawan mambobin ƙasashen da ake yi a cikin ƙasashen Turai ta Gabas, zai rura fitina da tashin hankali a yankin. Saboda haka da sun ji wannan gargaɗi kuma sun yi amfani da shi, ai da Rasha ba ta harzuƙa har ya mamaye Ukraniya ba.
Haka Ramaphosa ya bayyana a Zauren Majalisar Afrika ta Kudu, a ranar Alhamis.
Shugaban na Afrika ya ce ƙasar sa na mai ra’ayi da matsayar cewa ƙasashen NATO su daina yin barazana ko amfani da ƙarfi a kan wata ƙasa mai ‘yancin kan ta.
Ya ce ya na da muhimmanci a fahimci salsala da musabbabin yaƙin Rasha da Ukraniya, kuma a ɗauki matakan samar da zaman lafiya. “Saboda ba zai yiwu a zura ido ƙasashe na afka wa wata ƙasa da yaƙi ba.
Daga nan sai ya nuna cewa shi bai yarda da ƙaƙaba takunkumin karya tattalin arziki ba, domin babu wani tasirin da ya ke yi, sai ma ƙara tsawaita yaƙi zuwa zango mai nisa.
Ramaphosa ya ce wannan yaƙi ya ƙara nuna rashin ƙarfin faɗa-a-jin Majalisar Dinkin Duniya.”
“Ya kamata a yi wa Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya garambawul, domin ba ta dace da irin yanayi ko halin da duniya ke ciki ba a yanzu.”
“Babu wani amfani da Manyan Ƙasashen Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ke wa duniya, sai dai cimma burin su su-ya-su kaɗai.”
Ya kuma yi kira da a farfaɗo da Ƙungiyar ‘Yan Ba Ruwan Mu, waɗanda ba su goyon bayan aƙidun Amurka ko na Rasha, domin su tsaya tsayin daka wajen jaddada zaman lafiya a duniya.
Aƙalla mutum miliyan 6.5 sun rasa muhallin su a yaƙin Ukraniya, sannan kuma wasu miliyan 3.2 sun tsallake gudun hijira ƙasashen ƙetare.