Tsohon shugaban majalisan dattijai, Bukola Saraki ya bayyana cewa jam’iyyar PDP a shirye take ta amince da zabin ɗan takaran shigaban kasa daya idan hakan ya zama dole a tsakanin su.
Saraki ya bayyana haka a garin Bauchi a lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan Bauchi tare da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Dukkan su ukun wato Saraki, Balan Bauchi da Tambuwal duk ƴan takaran shugaban kasa ne a jam’iyyar PDP.
” Abinda ya kawo mu garin Bauchi shine don mu gana a tsakanin mu mu ga yadda za a yi a samu daidaituwa a tsakanin mu duka ƴan takarar domin samun matsaya ɗaya idan yakam ya taso.
” Domin mu samu hadin kai a tsakanin mu. Kasar nan shine a gaban mu ba son rai da burin kowanne ɗayan mu ba.
” Dukkan mu uku da muka bayyana ra’ayin mu na takarar shugabancin kasar nan, za mu iya dukkan mu. Amma kuma dole mu saka kasar mu a gaba kafin burin mubya biyo baya.
” Za mu ci gaba da tattaunawa a tsakanin fomin samun matsaya ɗaya a tsakanin mu sannan kuma za mu ci gaba da yin haka har sai mun iya cimma matsaya ɗaya a tsakanin mu tukunna domin Jam’iyyar mu da kasar mu baki ɗaya.
Discussion about this post