A cigaba da neman goyon baya da haɗin ka jama’a da sanata Uba Sani ya ke yi domin zama ɗan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023, ya ziyarci wasu ƙananan hukumomin jihar Kaduna a karshen wannan mako.
Kananan hukumomin sun haɗa da Zaria, Sabongari, Kudan da Makarfi.
A wajen wannan taro Uba ya jinjina wa mutanen yakin bisa nuna masa soyayya da suka a lokacin da yakai wannan ziyara.
” Ina son in tabbatar muku cewa mun shigs wannan takara da kyakkyawar niyya ce sannan kuma domin jama’ar jihar mu ta Kaduna. Za mu ɗora daga inda hazikin gwamnan mu Nasir El-Rufa’i ya tsaya domin cigaban al’ummar jihar Kaduna.
” Bayan haka Uba Sani ya miƙa godiyar sa ga wasu jigajigan ƴan Jam’iyyar APC da su tarbe sa sannan suka yi wannan zagaye da shi cikin natsuwa da ƙauna.
Cikin waɗanda suka yi jawabi a wuraren tarukkan a lokacin waɗannan ziyara sun haɗa da tsohon kakakin jihar Honarabul Bashir Zubairu, tsohon kakain Kaduna, Aminu Shagali da dai sauran su.
A cikin tawagar sanata Uba akwai shugabannin kananan hukumomin Kaduna ta Kudu, Jarimi, Lere, Abubakar Buba, Kubau, Bashir Zuntu da ƴan siyasa da dama.