Wani mai amfani da shafin Tiwita na zargin wai tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana goyon bayan sa ga dan takaran shugaban kasa Rochas Okorocha a Najeriya.
Wani bidiyo da aka yada a shafin WhatsApp ya nuna wai tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya nuna goyon bayan sa sa ga takaran Okorocha.
Bidiyon mai tsawon dakiku 30 ya nuna Obama da mai dakinsa Michelle suna zaune a wani abin da ya yi kama da wurin taro. Daga nan sai aka gayyace shi ya matso gaba domin kaddamar da wani Fasta na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa rochas Okorocha.
Rochas Okorocha sanata ne da ke wakiltar mazabar yamma na jihar Imo a majalisar dattijai ta tara. Shine kuma tsohon gwamnan jihar Imo.
Duk da cewa mun gaza gano tushen bidiyon. Shafin yakin neman zaben Okorocha na dauke da hoton da ake zargin Obaman ya bayyana s bidiyon.
Masu amfani da WhatsApp da yawa sun musanta sahihancin wannan bidiyon. “An yi editing ne. Obama bai ma san Rochas ba,” a cewar wani mai amfani da WhatsApp.
Jama’a sun yi ta tambayoyi makamantan wannan amma a takaice dai abu daya suke so su sani: wai shin Obama ya bayyana tutar yakin neman zaben Rochas domin ya nuna goyon bayan shi?
Tantancewa
DUBAWA ta gano cewa an gyara bidiyon ne domin ya yi daidai da labarin da ake so a bayar. Da gaske ne Obama ya halarci taron da ya bude wani hoto, a binciken da muka yi cikin manhjan tantance hotunan bidiyo na InVid mun gano cewa an dauki hoton Okorocha ne an dora a kan zanen hotonObaman da aka gabatar masa a shekarar 2018 a cibiyar gidan tarihin Smithsonian.
Ainihin taron da aka yi yana kan shafin YouTube din cibiyar Smithsonian tare da wannan bayanin:
“Gidan tarihin hotuna na kasa, Smithsonian na gabatar da hotunan Barack Obama da Mrs. Michelle Obama wadanda masu zane Kehinde Wiley da Amy Sherald suka zana. Masu jawabi sun hada da Tsohon shugaba Barack Obama, Mrs. Obama, sakataren Smithsonian David Skorton, darektan Smithsonian Kim Sajet da masz zanen Wiley da Sherald.
A karshe
Wannan bidiyo ba gaskiya bane. An yi amfani da na’aura ne wajen gyara hotunan domin yayi daidai da abinda ake so a yi. Hasali ma bincike ya nuna Obama bai ma san Okorocha ballantan ya kaddamar da Kamfen din sa.