Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ce kwazo da nunajarumta da mata ke yi a jihar Kaduna musamman wadanda suke aiki karkashin gwamnatin sa lallai akwai yiwuwar mace ce za ta dare kujerar gwamnan jihar a 2023.
Zango na biyu a mulkin gwamnatin El-Rufa’i zai kare a shekarar 2023 sannan a yanzu haka mataimakiyarsa mace ce.
Da yake ganawa da manema labarai ranar Talata gwamnan El-Rufai ya ce ganin cewa akalla kashi 50% na mutanen jihar Kaduna mata ne da kuma matasa, ga dukkan alamu dai mace zata iya zama gwamna a jihar.
Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da mara wa mata baya ganin cewa a yanzu haka ma akwai mata kwamishinoni dake aiki a manyan ma’aikatu a gwamnatinsa.
“Muna da tabbacin cewa idan aka bai mata damar yin aiki da nuna bajintarsu za su zarce maza nesa ba kusa. Shine ya sa mukan zakulo mata masu basirar gaske sannan mu basu dama domin aiki a jihar mu. Kuma ina tabbatar muku da cewa ba su bamu kunya ba.
El-Rufa’i ya ce jihar Kaduna na burin ganin duk wanda zai gaji kujerar gwamnan jihar idan ya sauka mutum ne da zai cigaba da rangada wa mutanen Kaduna aiki babu kakkautawa.
” Eh tabbas akwai wanda nake so ya gaji kujerata amma fata na shine mutanen Kaduna su hada hannu da ni mu yi ta addua Allah ya zaba mana shugaban da zai kawo ci gaba a jihar, mace ce ko namiji.