Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wahala ko tsadar takin zamani a ƙasar nan za ta zama tahiri, tunda Masana’antar Takin Zamani ta Ɗangote Fertilizer Plant zai fara aikin sarrafa takin zamani har metrik tan miliyan 3 a duk shekara na yuriya.
Da ya ke jawabi lokacin da ya ke buɗe masana’antar a yankin Ijebu Lekki a Legas, Buhari ya ce masana’antar za ta ƙara shiga gaba wajen tabbatar da muradin ganin cewa Najeriya ta dogara da kan ta wajen noma abincin ciyar da kan ta, samar da aikin yi, ƙarin samar da kuɗaɗen shiga na waje da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Shugaba Buhari ya jinjina wa Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote, saboda jajircewar da ya yi domin ganin ginawa da kafa masana’antar sun tabbata.
Ita Ce Ta Biyu Mafi Girma A Duniya:
Buhari ya ce Masana’antar Takin Zamani ta Ɗangote ita ce ta biyu mafi girma a duniya. Sannan kuma a Afrika ita ce ta ɗaya, babu kwatankwacin irin ta.
Buhari ya ce ya yi farin ciki ganin yadda Ɗangote ya zama gagara-gasa a ɓangaren takin zamani, kamar yadda ya zama gagara-gasa a ɓangaren siminti, wanda har a ƙasashen Afrika 10 ya kafa masana’antar siminti.
“Wanann sabuwar masana’antar shaida ce da ke nuna yadda Alhaji Aliko Ɗangote ke da tantagaryar kishi, da ƙaunar ganin ya inganta tattalin arzikin ƙasar sa da al’ummar ta.
“Ina fatan nan ba da daɗewa ba zan sake dawowa na buɗe Matatar Man Ɗangote a cikin wannan shekarar.” Inji Buhari.
Buhari ya ce Ɗangote namijin ƙwarai ne, ganin yadda a duk sana’ar da ya sa a gaba, to sai ya kai Najeriya sahun gaban kowace ƙasa a Afrika.
Bayan tashi daga taron, Aliko Ɗangote ya kewaya da Buhari ya ga irin aikin da ake yi wajen kafa Masana’antar Tace Mai ta Ɗangote.
Ciki manyan baƙi a wurin har da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Wannan masana’antar dai an kashe dala biliyan 2.5 wajen kafa ta, kuma duk a yanki ɗaya ta ke da Matatar Man Dangote, wadda ake kan aikin kammala ginin ta kan dala biliyan 15. Gaba ɗaya Dangote zai kashe dala biliyan sama da 17.5 kenan wajen gina masana’antar.
Discussion about this post