Wankin hula dai na neman ya kai jam’iyyar APC dare domin kuwa duka ƴan takaran shugaban jam’iyyar sun ki amincewa da zaɓin shugaba Muhammadu Buhari, wato Sanata Abdullahi Adamu.
Majiyoyi da dama da suka tattauna da PREMIUM TIMES sun tabbatar mana cewa lallai akwai fa sauran rina a kaba domin ƴan takaran shugaban jam’iyyar ba su amince da zaɓin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
” Bari in gaya maka ka sani babu ɗaya daga cikin ƴan takaran da ya amince da zabin Abdullahi Adamu wato zaɓin Buhari ya zama shugaban jam’iyyar APC. Saboda haka ina tabbatar maka cewa yanzu haka yan takaran sun ce kowa tasa ta fishheshi kawai. Iya ruwa fidda kai.
Sai dai kuma wani abu da PREMIUM TIMES ta jiyo shine ƴan takaran bau ji daɗin yadda shugaba Buhari ya yi musu a lokacin da ya gana da su bane.
Majiya ta shaida mana cewa bayan duka ƴan takararn sun hallara a fadar shugaba Buhar, sai ya karanta jawabinsa inda a karshe ya bayyana cewa yana goyon bayan sanata Adamu Abdullahi ya zama shugaban jam’iyyar. Daga sai ya kama gaban sa yayi tafiyar sa ya barsu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
” Wannan abu ya bata wa ƴan takaran rai. Wasu sun ce shugaba Buhari bai ɗauke su a bakin komai ba saboda haka sai sun ga abinda ya ture wa buzu naɗi a wajen wannan taro.
Bayan haka mun gano cewa ashe dai gwamnoni suma ba du son zaɓin shugaba Buhari, amma ba su iya cewa basu so a dalilin haka sai suna bi suna ziga ƴan takaran kada su amince a fito kawai a yi zabe.
Discussion about this post