Hedikwatar Hukumar tsaron ƙasa DHQ ta sanar cewa ‘yan ta’adda 47,975 da iyalansu sun mika wuya a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan daga watan Satumban 2021 zuwa yanzu.
Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka a Abuja ranar Alhamis da yake bada bayanai game da aiyukan rundunar daga ranar 10 ga Maris zuwa 24 ga Maris.
Onyeuko ya ce dakarun sun kashe ‘yan ta’adda 17, an kama 35, an kwato manyan bindigogi Kirar AK-47 guda 35 da sauran bindigogi.
Dakarun sun kuma kwato shanu 270, babura 3 da kekunan hawa 13 wanda ƴan bindiga suka sace.
Ya Kuma ce mutum 7,000 ‘yan kungiyar ISWAP da ‘yan Boko Haram sun mika wuya sannan sun ceto mutum 27 da aka yi garkuwa da su.
Daga nan Onyeuko ya ce a ranar 14 ga Maris ‘Operation Hadarin Daji’ ta yi wa ‘yan bindiga ruwan bama-bamai a kauyen Unguwar Adam dake karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina inda aka kashe ‘yan bindiga 27.
Dakarun sun yi wannan nasara ne bayan sun samu labarin taron da mahara sama da 50 da kwamandojin su za su yi a wani gari.
Ya ce daga ciki ‘yan bindigan da aka kashe akwai wani Malam Sule Dan uwan gogarman dan bindiga Lalbi Ginshima.
Onyeuko ya ce sojin sama sun kashe ‘yan bindiga da dama a maboyar su dake Magaba a jihar Kaduna sannan sauran ‘yan bindigan da suka gudu sojojin ƙasa sun bi sawunsu sun kashe su.
Ya ce sojojin sun kashe ‘yan bindiga 8, sun ceto mutum 56 da aka yi garkuwa da su sannan ta kwato makamai da dama.
Onyeuko ya ce ‘Operation Safe Haven’ sun kama barayin karafunan layin dogo, sun Kuma kwato motoci uku, mota mai kirar J5 daya da bindigogi biyu kiran AK-47.