Rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun tsinci gawar Bamise Ayanwole mai shekara 22 wacce aka yi garkuwa da ita bayan ta shiga motar haya kirar bus BRT a Legas.
Bamise ta shiga motar haya mai lambar rajista 240257 da za shi Oshodo bayan ta dawo daga Ota zata Ajah ranar 26 ga Fabrairu inda daga nan ba a sake ganin ta ba.
Kakakin rundunar Adekunle Ajisebutu ya ce rundunar ta tsinci gawar Bamise a tsakiyan gadan ‘Carter Bridge’ dake kauyen Ogogoro a tsibirin Legas.
Ajisebutu ya ce rundunar ta kai gawar wannan yarinya dakin ajiye gawa dake asibitin ‘Mainland’ sannan sun sanar da ‘yan uwan mamaciyan.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abiodun Alabi ya aika da sakon ta’aziyarsa ga ‘yan uwan mamaciyar sannan ya tabbatar cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin kama mutanen da suka yi garkuwa da da ita.
‘Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargin suna da hannu a kisar yarinyar.
A ranar Asabar din da ya gabata rundunar ta sanar cewa ta kama wasu mutum biyu wanda take zargin suna da hannu a kisan Bamise.
Rundunar ta bayyana cewa mutanen na tsare a ofishinsu sannan suna taya su da bayanai wajen gudanar da bincike.
Rundunar ta kara yin kira ga mutane da su taimaka wa ‘yan sandan da duk bayanan da zasu taimaka musu a binciken da suke yi