Majalisar Zartaswa ta amince a kashe Naira biliyan 1 domin sayen na’urar ganewa da tantance maƙaryaci ko bayanan ƙarya a Hukumar Hana Sha, Sayarwa da Tu’ammali da Muggan Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA).
Haka kuma a cikin waɗannan kuɗaɗen za a ware wasu a sayo tabarau mai iya gani a cikin dare ko a cikin duhu.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana wa manema labarai haka a ranar Laraba, bayan kammala taron Majalisar Zartaswa a Fadar Shugaba Muhammadu Buhari.
Yayin ganawar da manema labarai, Malami ya jinjina wa Hukumar NDLEA, kuma ya ce za a sayo wa NDLEA kayayyakin ne saboda ƙoƙarin su wajen kama masu safarar muggan ƙwayoyi zuwa cikin ƙasar nan.
A wannan gwamnatin dai NDLEA ta kama masu safarar muggan ƙwayoyi da dama. A cikin su har da dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Abba Kyari, wanda NDLEA ta zarga da haɗa baki ana shigo da muggan ƙwayoyi, sannan kuma ta zarge shi da kafa dabar masu shigo da muggan ƙwayoyi.
An kuma kama wani malamin addini da basarake duk a ƙoƙarin da NDLEA ke yi.
Lissafin Ƙididdigar Tu’ammali da Muggan Ƙwayoyi na 2018 ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya miliyan 14.3 ‘yan shekaru daga 15 zuwa 64 duk su na shan muggan ƙwayoyi.
Malami ya ce idan aka sayo na’urar tantance maƙaryaci da gilashin gani har a cikin dare, hakan zai ƙara taimakawa da sauƙaƙa wa NDLEA wajen aikin daƙile muggan ƙwayoyi a ƙasar nan.
Ya ce za a kashe Naira 498,850,000 wajen sayen na’urar tantance bayanan ƙarya.
Yayin da kuma za a kashe Naira 570,825,000 wajen sayen gilashin gani ko a cikin duhun dare.