Ana ƙara samun wasu bankuna a Najeriya da su ka bi sahun wasu, su ka rage adadin kuɗin da kwastoma zai iya biyan hada-hadar ta hanyar amfani da karin ATM ɗin sa ya canji dala da naira.
Bankunan sun shaida wa kwastomomin su cewa sun rage daga dala 100 zuwa dala 20 ko 50 a kowane wata.
Hakan na nufin idan mutum zai biya wani ciniki ta hanyar amfani da asusun ajiyar nairorin sa don ya sayi dala, to a wata ba zai yi canji fiye da dala 50 ba kenan.
Hakan kuwa ya faru ne saboda gagarimar matsalar dala da sauran kuɗaɗen waje da bankunan Najeriya ke fama da su.
Bankin UBA ne ya fara ɗaukar wannan mataki tun a ranar 24 Ga Fabrairu, inda ya sanar cewa kwastoma ba zai yi amfani da ‘Debit Card’ ya yi mu’amalar canjin dalar da ta haura 20 ba a cikin wata ɗaya.
“Amma kwastoma ya tuna idan ya na da asusun ajiyar dala ko fam ko Yuro, zai iya yin amfani da kuɗin wajen da ke cikin asusun ta hanyar biyan kuɗin wani kasuwanci ko hada-hadar da ya yi ta hanyar amfani da ‘Euro Card’, POS na ƙasa-da-ƙasa, ATM ko hada-hadar kuɗi ta intanet, wato ‘online’.
UBA a lokacin ya ce ga mai son buɗe asusun kuɗaɗen waje amma ba shi da shi, zai iya garzayawa kowane reshen bankin su mafi kusa da shi.
Sai kuma ga shi ranar Laraba Zenith Bank ya yi sanarwa cewa ya taƙaita hada-hadar biyan dala daga asusun naira zuwa dala 20 kaɗai a kowane wata.
Zenith Bank ya kuma dakatar da hada-hadar ATM da POS ta kuɗaɗen waje.
A ranar Juma’a sai First Bank shi ma ya bi sahu, inda ya sanar da cewa, “saboda halin da ake ciki na rashin tabbas ɗin kasuwa, ya rage irin wannan hada-hadar zuwa gejin dala 50 a kowane wata.
Wasu bankuna da dama sun bi sahu a ranar Asabar, inda su ka danganta matsalar da “rashin tabbas ɗin da tattalin arzikin Najeriya ya tsinci kan sa a yanzu.”
Bankunan da suka bi sahu sun haɗa da GTBank, Wema Bank da Union Bank.
Najeriya na fama da ƙarancin dala da sauran kuɗaɗen ƙetare. Kuma dama idan ba a manta ba, wata biyu baya Babban Bankin Najeriya ya sanar cewa daga 2022 zai daina sayar wa bankuna dala da Yuro da fam na Ingila.
CBN ya ce sai dai bankuna su riƙa sayen kuɗaɗen waje daga hannun ‘yan Najeriya masu shigowa da kuɗaɗen idan sun fitar da kayan Najeriya sun sayar a waje.