Dan takarar gwamnan jihar Kaduna, Mohammed Abdullahi Dattijo ya girgiza Kaduna inda dubban magoya baya suka ɗunguma zuwa sakatariyar jam’iyyar APC domin kaddamar da kansa ɗan takarar gwamnnan jihar Kaduna.
Sakatariyar jam’iyyar ta cika makil da masoya da magoya baya domin taya matsashin ɗan takaran murnar ƙaddamar da takarar gwamnan jihar.
Kafin a kaiga wannan rana sai da Dattijo ya zazzagaya kananan hukumomin jihar domin bayyana aniyar sa ga musamman dattawa da kuma masu faɗa aji da kuma neman albarkar manya.
Bayan haka ne a yau Talata, Dattijo ya ziyarci sakatariyar jam’iyar a Kaduna domin ƙarvar fom din takarar gwamnan Kaduna.
A jawabin da yayi a wajen taron, Dattijo ya ce lallai zai tabbatar jihar Kaduna ba ta saki layi ba daga turbar da gwamna Nasir El-Rufai ya dora ta akai.
Dattijo na daga cikin makusantan gwamna Nasir El-Rufa’i wanda ya ke bugun ƙirji da su. Ya rike mukamin Kwamishinan kasafin kuɗin jihar.
Bayan haka sai gwamna El-Rufai ya naɗa shi Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar daga baya kuma ya maida shi Kwamishinan kasafin kudin jihar a karo na biyu.
Discussion about this post