Jennifer Douglas, tsohuwar matar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ta tabbatar da cewa yanzu babu aure tsakanin ta da Atiku.
Cikin wani bayani da ta saki a ranar Talata, Jennifer wadda cikin shekarun 1980s wata fitacciyar wakiliyar gidan talbijin na NTA ce, ta ce igiyar auren su ta tsinke ne saboda takun-saƙa da rashin jituwar da ya kunno kai tsakanin ta da Atiku, dangane da ci-gaba da zaman dirshan ɗin ta a Landan, da kuma wasu dalilai.
“Babban dalilin da ya kawo rabuwar aure na da Atiku shi ne rashin jituwa saboda ci gaba da zama na Ingila. Saboda a can na ke zaune domin na riƙa kula da ‘ya’ya na da kuma wasu saɓanin da mu ka daɗe mun kasa sasanta su a tsakanin mu.
“Ni dai a yanzu na fi so na zauna kusa da ‘ya’ya na, domin su ma su san mahaifiyar su na raye, kuma su ma su na bukatar mahaifiyar ta su a kusa da su.
“Saboda sun tashi a Landan babu uwa kusa babu uba kusa. Sannan kuma ‘yar uwa ta wadda ke zaune tare da su, har ta kasance tamkar mahaifiyar su, ita kuma ta rasu.”
Jennifer ta ce wasu daga cikin makusantan Atiku irin su Peter Okocha, Ben Obi, Tunde Ayeni, Kaftin Yahaya da Ben Bruce duk sun yi ƙoƙarin sasanta su, amma abin ya faskara.
Atiku da Jennifer sun rabu babu aure a tsakanin su tun a ranar 26 Ga Yuni, 2021.
Dalilin Rabuwar Auren Atiku Da Jennifer:
An riƙa yaɗa ji-ta-ji-tar cewa auren Jennifer da Atiku ya rabu saboda Atiku ya yi sabuwar amarya. Atiku ya shafe sama da shekaru 20 ya na auren Jennifer kafin su rabu.
Cikin bayanin Jennifer, ta ce tabbas Atiku ya ƙara aure, ya cike ta huɗu. Amma kuma ta nuna bai yi laifi ba, saboda a matsayin sa na Musulmi, ya na da halin yin mata huɗu.
Duk da ta ce Atiku ya yi auren ba tare da ya sanar da ita ba, amma ta gayyaci Atiku da amaryar ta sa zuwa bikin auren ɗan ta cikin 2018. A 2019 kuma ta goyi bayan takarar shugaban ƙasa a kamfen ɗin Atiku.
Atiku Ya Nemi Ƙwace Kyautar Gidan Da Ya Ba Ni A Dubai -, Jennifer, Tsohuwar Matar Sa:
Jennifer ta ce wani saɓani shi ne yadda Atiku ya yi ƙoƙarin ƙwace wani gida da ya ba ta kyauta a Dubai. Ta ce yanzu lamarin ya na kotu, tun bayan da ya tayar da kyautar.
Haka nan ta ce hatta gidan da suka zauna a Asokoro ma Atiku ya ba ta shi, kuma sakataren sa ya sa ya rubuta mata takardun yarjejeniyar haƙƙin mallaka.
“Lokacin da na zo Najeriya cikin Satumba, 2021 na nemi ganin Mai Girma Atiku. Na ce masa ina son zuwa Dubai na karɓi gidan can da ya ba ni. Amma sai ya tafi ganin likitan sa a Jamus, ba tare da mun warware ko da matsala guda ɗaya ba.”
Jennifer ta ci gaba da cewa Atiku ya ba ta gidan Asokoro amma da ta zo sai ta taras ya kori dangin ta da ke zaune a gidan. “Dalili kenan da na zo Abuja cikin 2021 na riƙa kwana a otal.”
Ta ce da ta je Dubai, ta je gidan da Atiku ya ba ta. Lokacin ya na Jamus ya na jiyya. “Sai ya yi min saƙon tes cewa ya ji na koma gidan Dubai. To na tabbatar na killace masa kayan sa da ke ciki. Kuma ya ce ‘ina yi miki fatan alheri.’ Na tattara kaya na damƙa wa Raheem.”
Ta ce ita ba dukiyar sa ta ke faɗan neman mallaka ba. Haƙƙin ta kawai ta ke nema. “Domin da dukiya na ke son mallaka, ai da ban ba shi takardun gidajen sa na Yola da Jos ba. Na aika masa su. Amma har yau ba a je an ɗauka ba. Ko yanzu ake don karɓar takardun a iya zuwa a ɗauka.” Inji Jennifer.